'Yar Uwa Shin Ko Kinsan Tarin Sinadaran Dake Cikin Ɓawon Ayaba Kuwa?

'Yar Uwa Shin Ko Kinsan Tarin Sinadaran Dake Cikin Ɓawon Ayaba Kuwa?
 
 

Daga DOCTOR MARYAMAH

 
 
Ɓawon ayaba fa! Wannan da ki ke ganin bashi da alfanu, da zaran kin cire shi a jikin ayaba za ki jefar  da shi. 
 
Zo in gaya miki wani sirri, na tabbata ba zaki koma yada ɓawon ayaba ba.
 
Ɓawon ayaba yana gyara jiki, yana sa fuska ta yi kyau da sheƙi na ban mamaki, domin kuwa yana ɗauke da tarin sinadarin:  Carbohydrate, Vitamin B6, B16, antioxidant, mineral hade haɗi da magnesium wanda ba shakka binciken masana ya tabbatar da yana raya kwayoyin halittar jiki, ƙurajen jiki da dai sauransu.
 
Yadda zaki yi maganin yaƙunewar fuska, samun santsi, kyau marar algus.
 
 
Zaki samu ɓawon ayabarki mai kyau, ki nemi zuma da Lemon tsami.
 
Ki ɗauko ɓawon ayabarki ki matsa masa Lemon tsami akai, sa'annan ki zuba kan haɗin ɓawon ayabarki da Lemon tsami, sai ki goga a fuskarki ko jiki, idan ya ɗauki kimanin rabin awa sai ki wanke.
 
Ƴar uwa, na tabbata zaki ba ni labari.