Sanannen Malamin Addinin Musulunci nan Mai Wa'azi a kasashen Duniya Dan Asalin kasar Malaysia Dr. Zakir Naik, Zai gabatar da kasida a Garin sakkwato a Taron karshe da za'a gabatar a Babban Dakin Taro na Kasa da Kasa da ke Sakkwato.
"Taron Makon Danfodiyo na Shekara Kungiyoyin Addinin Musulunci karkashin Jagorancin Majalisar Hadin kan Samarin Musulmi 'NACOMYO' da hadin guiwar Majalisar Maimartaba Sarkin Musulmi, duk shekara suna shirya, taron ne da zimmar fadakar da Alummar Musulmi irin Ayukkan da magabata suka yi dan tunatar da Alummar irin Dinbin Ayukkan da suka yi, wannan ne karo na 10.
Shugaban kwamitin Shirye-Shiryen Kuma Mataimakin Shugaban zakka da wakafi na Duniya Kuma Shugaban Hadakar Kungiyoyin Da'awa na kasa DCCN Malam Muhammad Lawal Maidoki Sadaukin sakkwato ya ce taron karo na Goma ya kunshi Daurar karantarwa littafan Shehu da Almajirran sa, an Kuma shirya laccoci, muhawara da auna fahimta ga manyan makarantu dana kasa da su, akwai wakoki, cikin harsunan Larabci,Hausa da Turanci, kana an gabatar da Waazukkan dare ,da shiraruwa a gidajen Kafafen watsa labarai na jihar Sokoto na tv da Radio, domin Samar da Ilimi,Fahimta,Azama akan Malammann jihadi. Malammai cikin da wajen kasar nan za su zo domin gabatar da kasidu baban-daban.
Dan malamin Fariq zai gabatar da kasida a Jamiar Usmanu Danfodiyo da Kuma gabatar da babban kasida Mai taken Alkurani a Babban dakin taro na kasa da kasa da ke a Sakkwato a lokacin Taron Mai Martaba Sarkin Musulmi zai karrama wasu fitaccin mutane da yake yi na Shekara Shekara.
Dr. Zakir zai ziyarci jahohin Legos da Ilorin gidan mallam Alimi Almajirin Sheikh Usmanu Danfodiyo na Ilori.