ANA BARIN HALAL......:Fita Ta 52
ANA BARIN HALAL....
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe
Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
Idan kana/kina sha’awar:
_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._
_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._
_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._
_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._
_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
*Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t
*Page 52*
*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559
~__________~
Hafsy da Huda ce suka mana rakiya zuwa Abujah, mun isa lafiya muka samu Aunty B da Aunty J sunzo, tare suka sake gyara mun gidana da Heedayah, mun samu an mana abinci, ga drinks kala-kala da suka mana, heedayah ce tazo ta rungume ni, ga cikinta da bai wuce 5month ba ya fito ɗas da shi, bayan ta sake ni ne taje ta rungume Hudah, hararanta A.G yayi sannan ya wuce ciki, gaskiya gidan yayi kyau kuma ya tsaru sosai, ga wasu kaya da aka saka mun a gidan kaman ma sunfi na bauchi kyau, da yake jirgi muka biyo sai babu gajjiya a jikin mu, abinci muka haɗu mukaci da su, M.G suna tare da A.G a parlor, hira sosai mukayi da su Aunty, daga baya suka ce zasu tafi, sun so su tafi tare da hafsy amma A.G fir yaƙi, daga Hudah har hafsy yace a gidan zasu kwana, don heedayah taso su tafi gidanta da Hudah, kallo ɗaya A.G ya mata ta risina, ita dai Hudah murmishi kawai tayi tace wa Heedayah ta bari kafin ta taɗi zata zo mata, "dayake mijin ta ne ya kawoki ko"? Ya faɗa yana hararan Heedayah, ita dai miƙewa da sauri tayi tana girgiza mishi kai alaman a'a, shi kuma M.G dariya kawai yake don yasan darun A.G.
Da wuri su Aunty B suka mana sallama suka tafi, dukkan mu uku muna zaune a parlor bayan tafiyan su M.G ma, amma shi kuma A.G ya wuce ɗakin shi, abun gwanin burgewa gidan, gashi dai 2bedrooms ne, amma a mugun sake gidan, don ɗakun A.G yana parlor, shima bawai ƙofan cikin parlor kai tsaye bane, zaki bi wani ɗan corrido ne daga parlon sai ki samu ɗakin shi, tou duk abunda ake a parlor bazai dame shi ba, haka shi bazai takura na parlor ba, imda dinning section yake nan ƙofan shiga kitchen yake, akwai store mai ɗan girma a kitchen ɗin, daga nan zaka fice ƙofan baya, wanda tanan ma zai sadaka da gidan Heedayah shima ta nata kitchen ɗin, amma tsakiyan su akwai wani ɗan boysquater mai ɗauke da ƙaramin parlor da ɗaki ɗaya da store, a parlor zaki bi wani ɗan dogon corridor zuwa ɗakina, ɗakine babban gaske, ga toilet ga kuma wani ɗan ƙaramin ɗaki a cikin ɗakin, kaman wurin da zaki ajiye wasu kaya haka akayi wurin, idan baki son shirgi a ɗakinki, may be ma wata zata iya mayar da shi ɗakin yara ma, don zai ɗauku madaidaicin gado da sauran tarkacen gado.
Fitowan A.G ne ya nuna mana an ƙira sallan magrib, ido ya ƙura mun yna maida links ɗin rigan shi, miƙewa nayi ina faɗin, "bari mu tashi muyi alwala, ashe an ƙira sallah"? Lumshe ido yayi ya sake buɗesu akaina, batare da yace mun uffan ba ya maida kallon shi kan Hudah, "babu buƙatan wani abu ko"? Sannan ya ƙure hafsy ma da kallo, jiran ko da mai buƙata a cikin su, murmushi hafsy tayi ta juya kanta alaman babu komai, sannan ta miƙe hanyar nawa ɗakin tana faɗin, "sai ka dawo Yayah", amsawa yayi sannan ya ƙure Hudah da ido, itama murmushi tayi tace, "Yayah babu komai, komai da muke buƙata naga sun kawo, sai ka dawo Allah ya tsare", ta faɗa tana juyawa hanyar ɗakina.
Giran shi ya ɗaga mun duka biyu, alaman nifah? Murmushi nayi nace, "babu komai Jarumina, fatan kadawo mun lafiya kawai damuwa na", na faɗa ina kallonshi ina ɗan rakuɓewa gefe kaman munafuka.
"Jarumi ko"? Sannan ya lumshe ido ya buɗe, "Jarumin ki ko? Lallai da magana, bari na dawo kimun bayanin jarumtar A.Gn ki yarinya".
Baki na ɗan rufe kaɗan da hannu na ina dariya, "nifa bana nufin komai ranka ya daɗe kawai dai...... Kawai dai fatan ka dawo lafiya ne nima nayi maka", na faɗa ina dariyan shi, shima dariyan yayi mai kama da murmushi ya wuce waje, domin ƙiran shi da naga M.G yayi ta waya, bai ɗauka ba kawai ya duba ya mayar da wayan cikin aljihun shi.
Ɗakina su Hudah suke shirin bacci, ni kuma na gajji da mitan Hudah akan na tafi wurin ɗan'uwanta na bar shi shikaɗai, ita dai hafsy tana kwance rub da ciki tana ta wayanta da yayah ishaq, kaman munafuka ko muryanta baka tsinta, haka na shige toilet nayi wanka da ruwa mai zafi, bayan nagama na fito na shiryawa cikin wani rigan bacci red colour, rigan dogone ya ɗan wuce gwiwa na kaɗan, amma kuma hannun shimi ke gareshi, gaban rigan gaba ɗaya net ne, gashi yana da alaman gidan bra, magani na nasha wanda hudah ta sake jaddada mun, nasha nayi hayaƙi, na kuma shafa na shafawa, daga baya nasaka rikan bayan na jira ƙaurin jikina ya ɗan rage, hijab ɗina na ɗauka har ƙasa na saka, sai da safe nayiwa Hudah, hafsy kuma mari na ɗaka mata a cinyoyinta na fice.
Ido ya ɗago ya ƙura mun tunda na shigo parlon, nima idon na ƙura mishi bayan naja wuri guda na tsaya, ganin haka ya saka ya buɗe dukka hannayen shi, "ki matsar da wannan abun jikin kin kafin ki ƙaraso nan baby girl",
zare hijabin nayi idona yana kanshi, akan kujeran da yake gefene na ajiye, sannan na sauƙe ajiyan zuciya mai ɗan ƙara kaɗan ganin yadda A.G ya wani lumshe idanun shi kaman ba zai iya ganin mutum ba ya ƙura mun, hannun shi ya ƙara buɗewa yana mun alaman na ƙarasa wurin shi, nidai cike da tsarguwan warin hayaƙin da jikina yakeyi na ƙarasa, kan cinyar shi ya zaunar dani, dama ya cire rigan shi sai wani white singilet ne ajikin shi, sai dogon wandon shi, zama nayi sosai akan cinyan shi, shi kuma yasaka hancin shi yana shinshina wuya na, abun har mamaki yake bani, ni da nake warin hayaƙi shi kuma yana wani shinshina ni, da ƙyar na samu ya iya tashi muka wuce room ɗin shi, muna shiga ya kwantar dani ya wuce toilet ɗinshi, ya daɗe sosai sannan ya fito yana ta zabga ƙamshin shwer gel ɗin dayayi wanka da shi, shiryawa yayi gaba ɗaya hankalinshi ya tafi kaina, hmmmm Aunty nice A.G nah nace miki duniya ne, babu wata ƴa mace inaga a doron duniya da tayi dace da miji mai tsananin sonta ba irina, gaskiya A.G ƙarshe ne a nuna so, ashe dam haka sirrin auren shiru -shirun namiji yake? Wato Aunty nice babu dare ko rana da A.G zai kasance dani bakiji yana kuka ba, kuka kuma da hawayen shi, wani sa'in har tsoro nakeji naga kaman suma zai mun idan yana kwance dani, kuma hakan sai na lura nima wani shauƙi sosai ya ke sakani, ji nake babu wata mace da ta fini dacewa da miji a duniya".
nidai murmushi nayi ina ƙara maida kaina da nutsuwana kan Hajiya Aysha mayar A.G uwar Nana khadijah (Mamah)
A zuciyata kuma nace naki kika sani nima haka nakeji nawa Gwarzon yafi naki iya nuna mun so da kulawa, don kawai ....... Kawai dai shikenan, na faɗa a zuciyata, a fuskana kuma na bita da murmushi, ina ƙura mata ido, idan kuma nayi ƙarya ku tambayi , *sahibata ummie yawale* nima tasan irin son da nawa mijin ya mun, wane wani A.G .
Hudah da hafsy sun mana 2weeks, da ƙyar A.G yabar Huda taje gidan M.G tayi 2dys, Shima sai da yaga ran M.G ya ɗan ɓaci ne, don yace idan yana ganin gidan heedayah gidan ƙanwarta ne, wato shi ba yayan huda bane shi bare ne ko? Shi bai wani ɗauka ta wurin yayan shi mijinta ba, shima ae ɗan daddy da mummy ne, amma idan A.G ya cire shi babu komai Huda basai tazo gidan shi ba, ganin yau ɗaya M.G ya nuna ɓacin ranshi yasaka yace taje tayi 2dys, hafsy kam dama 5dys tayi a gida na ta ɓalle chan gidan su yayah, wai a cewar ta da zaran A.G ya shigo tou bata wani ƙara ganina, wai bana bata kulawa, kaji sharri irin na autar ummie, naji daɗin zama dasu wallahi, da zasu tafi duk sai naji kewar su ya ishe ni, amma babu yadda na iya haka suka tafi, tare da M.G da kuma yayah Ahmad suka tafi, mota suka bi a komawar su, A.G nah yana fita office kuwa heedayah take shigowa, biyar nayi take guduwa nata gidan, gashi cikinta mai ƙin yin girkine, Allah yasota M.G baida fitinan sai tayi kaza tayi kaza, bata ma yin girki banda breakfast, Ni nake mana taci ta tafi da na M.G, gashi bai ma yawan zama a Abujah yanzu sosai, kullum yana hanyar lagos, yakanyi 2weeks a chan kafin yazo yayi 5dys haka a Abuja.
Bamufi 2month da dawowa ba nafara laulayin mai zafin gaske, gashi ya sakani wani irin shiru da rashin son cin abinci, A.G yayi fama dani akan abinci amma fir naƙi, saidai zan wuni ina shan ruwan tea, shima black tea, a haka har na shiga 3month, lokacin heedayah tana 8month, wata rana A.G ya fita da wuri shida Yayah Ahmad, kasa tashi nayi na mishi ko ɓreakfast, shima bai wani takurani ba, fita sukayi bayan ya jaddada mun nine nayi na tashi nayi wankan magani nasha tea, da ƙyar na amsa mishi ya fice, daga nan kuma Heedayah ya tattaro yace ta dawo parlor na ta zauna, idan nine yayi ta tasheni nayi wanka nayi break, haka doe tazo ta kwanta a parlor tana kallon dole, don ba gwanar kallo bace ita sai yawan son karatun hausa novel, inda muka ƙara ƙullewa da ita ma kenan, duk da A.G baya son karatun haka ya barni.
Bacci na nakeyi cike da wasu birkitattun mafarki, a haka nayi mafarki wai gani nan a garin bauchi ina kwance a ɗakin hajiya ummah, kuma alama ya nuna kaman ina gida lokacin banyi aure ba, amma ka ina kwance da ciki a jikina rusheshe, ina so na tashi amma kuma na kasa, chan sai naga ƙofa ya buɗe wata mata mai fuska a rufe da wani abu ta shigo, hannunta ɗauke da wani jaririn yaro fari sol an mishi kwalliya, kyaun yaron sai ya mun kaman fuskan A.G, duk sai naji hankalina da ƙauna na ya koma kan yaron, yana ta wasa da hannayen shi da ƙafafun shi, chan sai naga matar ta yaye abunda ya rufe fuskan ta, kawai sai naga fuskan mamie tana mun wani dariya har da hawayenta, tana kuma nuna mun fuskan kyakkyawan yaron daya ƙura mun ido yana kallona kaman ba baby ba, gashi fuskan sak na A.G, amma kuma yana so yayi kuka alaman wurina yake son zuwa, "kina son ki karɓi yaron ne"? Naji muryan ta tana tambaya na, daga bayanta kuma sisto na habiba ce take mun alaman a'a da kanta, ita kuma tana riƙe da ƙofa tana kokiwan shigowa amma sai naga an figo ta ta koma baya, chan saiga Raliya da surkuwarta sun shigo suma suma dariya, hannu na miƙa don na karɓi jaririn da yake ƙoƙarin miƙo mun hannunshi, kawai sai naga sun haɗu su uu sun koma mutum ɗaya amma da fuskan mutum uku, wato mamie, raliya, surkuwata, jeho mun babyn sukayi ya faɗo jikina, abun mamaki duk kyaun da nagani da fari a tare da yaron sai ya juya mun baƙiƙirin da suka jeho mun shi kan cikina, kuma hannayen shi duk sun watsu a jikina kusan guda goma ko fi, don ko ta ina sun manne a jikana, gashi ya wani ƙamƙameni yana ƙyalƙyalah dariya irin yadda suma sukeyi, aiko banbi takan nayi addu'a ba kawai sai na zabga wani rin ihuu mai ƙarfin gaske, daidai lokacin kuma naji na farka da wani uban ƙara a bakina, ga zufa daya gama wanke mun jiki kaman wanda nayi tsere, ina tashi zaune kuma saiga Heedayah ta faɗo ɗakin da saurinta, jikinta duk rawa yake tazo ta rungumeni a jikinta.
Jinta a jikina nima nayi saurin rungumeta ina kuka, gashi gaba ɗaya illahirin jikina rawa yakeyi, inda mamie suka tsaya na ƙurawa ido, amma sam babu kowa ballantana komai, "meya faru Aunty kike ihu"? Heedayah da duk hankalinta yake tashe ta tambayeni, jikina da muryah nah gaba ɗaya rawa sukeyi, da ƙyar na buɗe baki nace, "zuwa sukayi suka bani tsoro da jariri", ina gaya mata abunda ya faru duk ta wani firgice, da sauri ta ɗauki waya ta ƙira A.G nah, sun riga da sun fita a gari shida yayah Ahmad, suleja sukaje Domin zasu gana da wani mutum daya nemi su, umurni ya bata da na tashi ta taimaka mun nayi wankan maganina, kuma ta tabbatar nasha tea da bread, kuma kada ta yadda su kunna kallo idan ba karatun qur'ani ba a gidan, haka akayi wanka ta riƙe ni akan na tashi naje nayi, ai kuwa kaman jira ake naje daidai ƙofan toilet ɗin sai naji wani iein mummunan murɗawan ciki mai azaban gaske, hannun ta na riƙo da ɗan ƙarfi na runtse ido na, chan sai naji abu shaaaa ya zubu mun ta ƙasa na kaman wani ruwan naƙuda idan mace zata haihu, dagani har uta muka ƙurawa ruwan da yake zuba kaman wani fitsarin sati guda na riƙe.
Sai da ya gama zuba tukun naji na fara jin wani azababben ciwo a marana, amma haka muka ƙuƙuta muka shiga toilet ɗin, da ƙyar na samu na tsaya, ai kuwa tana fita naji marana yayi wani mummunan ƙullewa, sunanta na ƙwala ƙira da ƙarfi, da shigowanta da ɓalluwan jini a jikina duk lokaci ɗayane, daga nan sai naga toilet ɗin yana mun duhu, ɗif kuma sai naji komai ya tsaya mun.
Cikin sauri yau nake rubutun nan, hala kuyita karo da errors
*AUNTY NICE*
managarciya