Dan majalisar dattijai mai wakiltar yankin Sakkwato ta Gabas Sanata Ibrahim Lamiɗo ya nuna takaicinsa kan yadda tsaro ke taɓarɓarewa a yankinsa kullum, abu ne da yakamata masu kishin al'umma su yi ta faɗakar da gwamnati don samun nasara kawar da matsalar tsaro da hana yankin cigaba.
Sanata Ibrahim Lamiɗo a hirarsa da manema labarai a Sakkwato ya ce "maganar gaskiya Gabashin Sakkwato na fama da matsalar tsaro ba sauki a yankin, matsalar ta ƙara yawa ba wata rana da ba a shiga wani ƙauye ko a kashe mutane, ko sace su, muna cikin damuwa kan matsalar tsaro."
Kan maganar ƙoƙarin da yake yi na ganin a samu tsaron ya ce "samar da tsaro abu ne da ya shafi al'umma da gwamnati amma ta gefe na Allah ya sani, jama'a sheda ne, na ba da tawa gudunmuwa sosai a harkar tsaro, bayan mun samu haske kan Civilian JTF da muka kawo, naga yakamata mu ƙara yawansu, sai wasu 'yan siyasa da ba su son a kawo jami'an suka kawo mana cikas, amma ban haƙura ba zan bi hanyoyin da nake iyawa da su saɓawa doka ba, naga an kai jami'an a ƙaramar hukumar Raɓah da Sabon Birni da izinin Allah sai an yi masu sansani don mutane su samu saukin rayuwa."
"Ina jajantawa 'yan uwana da ke yankin Sakkwato ta Gabas da harin 'yan bindiga ke cigaba da hanawa walwala da mayar da su marayu, mata kuma zawarawa, Allah ya ba mu haƙuri ya isar mana kan abinda ke faruwa, waɗanda ake haɗa baki da su wannan lamarin, Allah ka sansu ka yi mana maganinsu,"kalaman Lamiɗo.
Kan yadda su yan siyasa ke rungume hannaye sai ta'adanci ya faru su je jaje ya ce "waɗanda suka rasa haifansu ba kuɗi da abinci suke buƙata ba, abu mai muhimmanci a ƙara inganta harkar tsaro don in ka ba shi abinci yau, gobe da jibi kai za ka bashi ne, amma in sauƙi ya samu kowa shi zai je ya nemi abincinsa, ni ban ɗauki haka matsayin tausayawa ba, kai ƙarshen lamarin matsalar tsaro shi ne tausayawa al'umma don su je su yi noma," Sanata Lamiɗo.
Yankin Gabascin Sakkwato yafi kowane yanki a jihar tagayyara a lamarin, an yi kisa da sace mutane da kore gari gaba ɗaya, har yanzu babu ƙididdigar adadin waɗanda suka samu matsala kan tsaro a yankin, kullum gwamnatoci alƙawali suke yi na inganta tsaro a yankin amma dai ba a cimma lokaci ba.
Harkar noma da kasuwanci da karatu sun tsaya cak a yankin abin da mutanen yankin a kullum suke kokawa gwamnati na ta duba halin da suke ciki.
Da yawan mutane a yankin sun ce da gwamnati za ta haɗa kai da Sanata Lamiɗo a yi aiki tare da za a iya samun nasara kan lamarin domin tunaninsa kan magance matsalar tsaro, kwalliya na iya biyan kuɗin sabulu in aka bi.
Sun yi kira da a samar da haɗin kai a tsakanin ɓangarorin gwamnati a yaƙi lamarin domin ana cikin musiba kan matslar a yankin da jiha baki ɗaya.