Hanyoyin Magance Matsalar Tarbiyar Yara A Wannan Zamani
Iyaye na taka muhimmiyar rawa ga tarbiyar yaran su, ta hanyar sanar da su banbancin dabi’u masu kyau da marar kyau, amma yanzu iyaye a ganina, sun yi watsi da wannan hakkin daya rataya a wuyansu. Ana yawan saka yara Makarantun boko dana Addini, wasu daga ciki tun safe idan yaro yaje sai marece zai dawo, koda zai dawo gajiya ta masa yawa, suma iyaye idan dukkansu aiki suke da baya basu damar dawowa da wuri, ba su da lokacin bincikar litattafan yaran su da kuma kokarin fahimtar yanayin da yaran nasu suke ciki, a lokacin da suka dawo daga makarantar. A wannan bangaren kuma, ba aiki kadai ne ke shiga gaban iyayen yanzu ba, domin yanzu akwai kafafen sada zumunta na zamani, irinsu Watsapp, Facebook, Twitter da sauran su, da iyaye Mazan da Mata suka mai da 'Armun Azimun', wadanda mafi yawan lokutta su ne ke dauke masu hankali, daga kan iyalansu.
A wannan zamanin da muke ciki, tarbiyar yara sai dada gurbacewa take, wanda ya sa mutane ke tunanin ina muka dosa.
Wasu kananan yara ba su san darajar malamansu, makwabtansu, dama danginsu ba, saboda wannan lokaci sai ka ga ka yi wa yaro karami Magana akan wani abu da yake na kuskure ya mayar maka ko kuma yaki daina abin da yake, idan ka matsa kuma sai yace kai ba uwarsa ba ba ubansa ba, wane hakki kake da shi nason takurawa rayuwarsa.
Kananan yara yanzu sai ka ji zagi iri-iri daga bakunansu masu munin gaske. Wayoyin zamani suna daya daga cikin abin da ya taimaka wajen gurbace tarbiyar yara, ta hanyar shiga yanar gizo da suke suna kallon abubuwan da ba su dace ba, masu cike da batsa , tare da koyon munanen dabi’u iri-iri, al’amarin sai dai muce Allah ya sauwaka, ya kawo mana dauki.
Abin tambaya anan shi ne meke jawo hakan? Kuma ina mafita? A tunani na , idan aka ce tarbiya, musamman ta karamin yaro, toh wuri na farko da za’a fara dubawa shi ne iyaye, domin iyaye musamman iyaye Mata da nauyin yafi rataya akan su kamara yadda Hausawa kance , ‘’Su ne makaranta ta farko, a Duniya’’.
Iyaye na taka muhimmiyar rawa ga tarbiyar yaran su, ta hanyar sanar da su banbancin dabi’u masu kyau da marar kyau, amma yanzu iyaye a ganina, sun yi watsi da wannan hakkin daya rataya a wuyansu. Ana yawan saka yara Makarantun boko dana Addini, wasu daga ciki tun safe idan yaro yaje sai marece zai dawo, koda zai dawo gajiya ta masa yawa, suma iyaye idan dukkansu aiki suke da baya basu damar dawowa da wuri, ba su da lokacin bincikar litattafan yaran su da kuma kokarin fahimtar yanayin da yaran nasu suke ciki, a lokacin da suka dawo daga makarantar.
A wannan bangaren kuma, ba aiki kadai ne ke shiga gaban iyayen yanzu ba, domin yanzu akwai kafafen sada zumunta na zamani, irinsu Watsapp, Facebook, Twitter da sauran su, da iyaye Mazan da Mata suka mai da 'Armun Azimun', wadanda mafi yawan lokutta su ne ke dauke masu hankali, daga kan Iyalansu.
Sai kuma makahon so da Iyaye ke yiwa yaran nasu, wanda ke sa ba sa kula tarbiyarsu yanda yakamata.
- Na farko, ba su ganin laifin yaran nasu, idan sun aikata ba dai-dai ba.
- Na biyu, idan ma sun fahimci girman laifin da yaran suka aikata, basa iya hukunta su, yadda ya kamata.
- Na uku kuma, wani baya da damar hukunta yaran su ba tare da sun ga laifin sa ba, ko kuma sun nuna rashin jin dadin su akan yin hakan, sabanin inda aka fito, wanda mu Iyayenmu ba haka suka tarbiyantar da mu ba.
Da fatar wannan ‘yar gajeruwar tunatarwa game da yanayin da tarbiyar kananan yara take ciki, za ta yi tasiri a zukatan Iyaye, su kuma dauki matakai da za su kawo mafita ga wa’ennan matsalolin. Allah ya kara shiryar damu baki daya, ya kara bamu ikon babanta gaskiya da karya. Allahumma ameen.