ANA BARIN HALAL.....
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin ƘarfeBurin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_
*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*
*Page 53*
Lokacin dana dawo hayyaci na sai na samu kaina kwance a gadon asibiti, gefe na A.G ne zaune ya yi tagumi, yayah Ahmad kuma tsaye ya rungume hannayen shi a ƙirji, heedayah kuma zaune ta buga ubantagumi, da sauri A.G ya matso kusa dani, daidai kuma Aunty B na fitowa daga toilet ɗin ɗakin, "beauty sannu", naji muryan shi kaman wanda zaiyi kuka ya furta, matsowa yayah Ahmad yayi kusa damu, shima sannun ya mun, nidai ido kawai na bisu da shi, chan kuma na lumshe ido na nayi shiru, inajin yayah Ahmad nagayawa Aunty J a waya na farka, wanda daga dukkan alamu ita tana gida ne, gefe na Aunty B tazo ta zauna, hannun ta tasaka ta riƙe hannu na tace, "bestyn besty kin tashi? Sannu ko besty".
A.G Dr ya ƙira a waya ya gaya mishi, babu daɗewa nurse ta shigo ɗauke da tray ɗin sun nan, ita da Aunty B suka taimaka mun na tashi muka shiga toilet, wato daga dukkan alamu nasamu misscarrige, mummunan tashin hankali naji ya sameni, amma na ɓoye don kada su fahimta nai kunya, haka suka tayani nayi wanka, gyara jikina nayi da pad, muna fitowa Aunty B ta bani tea mai kauri wanda na samu heedayah na gaurayawa, hannu na saka na karɓa, ina zaune a bakin gaɗon ƙafana suna ɗaure akan kujeran da A.G da ya zauna,shi kuma yana zaune a gefe nah ya doka uban tagumi.
Allura nurse ɗin ta mun da wani magani , bayan ta gama ta fice a ɗakin.
2hrs na ƙara aka sallame mu, bayan mun shiga Dr yayi mun scarning, inda naji Dr yana yiwa su yayah da A.G bayanin cikin gaba ɗaya ya fice ba sai anyi wankin ciki ba, jiki a sanyaye A.G ya amsa mishi, sannan ya bamu takaddan maganin da zamu saya.
Gida na muka taho tare dasu, bamu daɗe ba Aunty J tazo tare da Areefh ta kawo abinci, suna nan a gidan dukkan su har 10:00pm, munyi waya da su ummie, Aunty Rakiya, mummy, hajiya ummah, hattah Abbana da Daddy sun ƙirani, a gidan Aunty B ta kwana da ni, kuma inaji hajiya ummah tace kada ta barni nasha ruwan sanyi kuma nayi wanka ko na sati biyu ne zuwa uku.
Washe gari kuwa Abba na ya shigo ya duba ni, inda yace daga lagos yake, kuma gobe zai wuce bch, idan yaje ummie zasu zo su dubani, nidai ranan farin cikin zuwan Abba na kaman zanyi yayah, da zai tafi kaman zanyi kuka yana riƙe da hannu na har jikin motan shi muka raka shi, a kunne ya sunkuya ya gaya mun "insha Allahu sisto zan dinga zuwa dubaki idan kinyi murmushi", ae kuwa dariya na ƙyalƙyale da shi, hakan kuma ya saka shi shima yin dariyan su yayah suna taya mu.
Bayan kwana 2 da faruwan haka kuwa sai ga su ummie da mummy, hajiya ummah da Aunty Rakiya sun zo, naji daɗin ganin du ainun, da suka shigo na rasa wurin wa zanje kawai sai na rufe fuskana da hannu na ina dariyan daɗi, don babu wanda yace mun zasu zo, mummy naje na fara hugging tana dariya na ita ma ta rungumo ni, hajiya umma ta turo baki gaba tana , "don Allah ja jiki da munfurcinki yarina, nidai ku bani wuri na zauna kada kayan takaici ya kaini bango, nasan da ba don ganin idon surukuwar ki ba nuna mana zakiyi bamu taɓa haihuwa ba, uwarki zaki runguma, kaman mu bamu da yara Allah na gode mishi ma da ya bani usmanu, ɗaya tamkar da dubu" riƙo hannunta yayah Ahmad yayi yana zaunar da ita akan kujera, cikin muryan shi marar hayaniya yace, zaunawar ki lafiya uwar usmanu", dole ita ma tayi dariyan, bayan duk sun zauna na koma daf da Aunty rakiya na zauna akan cusion da yake ƙasa a wurin, gaishe su nayi ɗaya bayan ɗaya, sannan suma suka mun yayah jiki, duk ido na ya na kan ummie nah, itama muna haɗa ido take sakar mun da murmushi.
Shigowar heedayah ne ya mayar da hankalina kanta, tana tura ciki gaba ta rungume mummy tana dariya, ita daga alama bata san da zuwan su ba sai yanzu, abun karyawa Aunty B ta fito musu da shi, saboda isowan ƙarfe 9 sukayi, dayake flight ne, saboda kada uwar usmanu ta gajji a mota, ɗakina ta wucewa su mummy da ummie, Aunty Rakiya dai tace a barta tare da ummanta, A.G sun fita tare da yayah, ɗaki heedayah ta bisu, nidai ina xaune tare da su, nima tare da su mukayi break ɗin.
Naji daɗin zuwan su, duk da ummie na bata kwana gida na ba, chan gidan su yayah suka tafi tare da Aunty Rakiya, hajiya ne ta kwana mun duka biyun da sukayi, mummy ma kwana ɗaya tayi taje gidan M.G, duk da A.G yaso yi mata gardama amma tace ae chan ma gidan ɗanta ne, kuma ranan M.G ɗin ya dawo, babu yadda ya iya haka taje.
Ranan Laraba Suka koma, haka kuma bayan nayi 2weeks Aunty B ta tafi, naso na kara jin karfin jikina ba tare dana komawa A.G ba, amma kaman yana jiran tafiyan Aunty B ne ya ƙiya mun, dayake jinin baifi kwanki kaɗan ba ma ya tsaya, tou Allah ya so Aunty ta ɗan mun gyara ba mai tsananin yawa ba, dahuwar kaza na nonon raƙumi, da gumba sai wasu da zansha da nono ta saka wata mata ƴar sudan ta mun, ga kuma dahuwar wani kazan kaman gasa shi akayi da maganin ajiki, kaman dai irin anyi tukunyan nan da shi, haka kuwa nasha gumurzo a hannun jarumin mijina.
Babu wuya wurin ubangiji, ranan 10/08/2022 heedayah ta haifi ɗanta kyakkyawa mai kama da M.G, lafiyayyen yaro mai kyawawan ido irin nasu heedayah da jarumina, don idan ka kalli yaron zakace sak M.G, idan ka matsa kuwa sai kace gidan su maman shi ya biyo, amma a zahiri farin shi da siffanshi, da kamanin hancin shi da komai irin na M.G ne, amma ƙwayyar idon shi sak nasu A.G da su heedayah ne, yama fi kama dana A.G, ranan farin ciki kaman zai huda zuciyar mu, A.G yaje bauchi akayi haihuwar, saboda haka ranan gaba ɗaya tarewa nayi a gidan bayan an dawo daga asibiti, kuma gaskiya daga Aunty B har Aunty J sunyi kara sosai wa A.G da M.G, don abunda zasuyi idan ni na haihu tou haka sukayi wa Heedayah, sun yi komai a mutumce, muna dawowa gida Aunty B ta ƙira wata ƴar'uwarta babbar matace da take zaune a suleja tazo har gida ta wanki yaro tsaf, fararen kayan sanyi aka sake saka mishi, sai naga ya ƙara wani haske da aka mishi wankan, nono aka saka heedayah ta bashi, da ƙyar ta yarda tasaka mishi nonon, don sai da Aunty j tayi da gaske da ita, yana kamawa kuwa ta fara kuka, nidai banda dariya babu abunda nakeyi, harara na Heedayah tayi tana jijjiga kai, "wallahi Aunty na lura tun kafin na haihu kike mun dariya, Allah kaɗai yasan ke me zaki aikata, gara ni ma halah", ta faɗa tana ƙara matse idonta don yadda babyn ya kama kamam ya shekara a duniya da ƙwarewa, nidai dariyan na sakeyi ina kallonta nace, "nifa kin san me yake sakani dariya ne? Tou matar da take cikin labour me ya kaita salati da kuma waƙa a lokaci ɗaya, ni shiya ɗaure mun kai, dama ana haka ne"? Na faɗa ina dariya, dukkan su dariyaɓ suka ƙyalƙyale da shi, hattah ita kanta mai haihuwar dariyan abunda tayi takeyi, "Allah ya nuna mana naki yarinya, hala ma pareri zakiyi" Aunty J tafaɗa tana zama bakin gadon, nidai karɓan babyn nayi na ƙura mishi ido ina murmushi, "ni wallahi kada ace nayi son kai, nidai yaron nan kyaun miji na ya ɗauko wallahi, jibi da ya buɗe idon nan kaman na Jarumi na, kai Masha Allah", na faɗa ina yiwa babyn kiss a fuskan shi.
"Chabb kaji wani zance, kina ga yaro ya ɗauko kyaun baban shi zaki wani haɗa shi da mijinki mai ɗaurarren fuska? Nidai ɗana kyaun Giwa na ya ɗauko", heedayah ta faɗa tana wani fari da ido, bakina a buɗe ina kallon ta, dariya su Aunty suke mana, wato kowa nata gwanin ne kyakkyawa.
(Na manta ko na gaya muku Aunty J ta haihu itama? Tana da yaro namiji, yanzu kuma dukkansu suna ɗauke da ciki ita da Aunty B, ita Aunty J lokacin da Ayshaa tayi ɓari cikinta ya kai 3month, so yanzu cikinta 5month, ita kuma Aunty B yanzu ne take cikin na, 3month, ita kuma ayshaa na maƙale da ɗan 2month, wanda daga ita har A.G alokacin basu da labarin shi, don tunda tayi miscarrige bata sake ganin period ba, so batayi tunanin ciki bane a lokacin, don bai nuna alaman komai ba da za'a gane).
Bayan 2dys A.G ya dawo, kuma ya dawo tare da wata umman mummy ce, wanda zata zauna da heedayah,matsayin kaka take a wurin du A.G, mace cr mai kirki, ga tsabta, ga ta da kazarkazar kaman mummy da heedayah, tunda tazo wancan matar da Aunty B ta kawo ta koma, Aunty j kusan kullun sai tazo duba heedayah, kuma takanzo da abinci, Aunty B dai cikinta da laulayi, so bata zuwa, bata ma sake zuwa ba sai ranan suna, shima sai yammah sosai tazo.
Ranan suna yaro yaci sunan *MUHAMMAD AUWAL* sunan babban yayan su M.G inda naji M.G yace yayan shi ne kuma Baban shine, a wannan ranan naga kara da zumunci na ƴan'uwanta ka, domin matar Yayah Auwalu ne kawai da basu ƙasan ba suzo ba, amma naga matar yayah sanie, rabiu, hassan da hussain, duk da dama Huda kam tamuce, babu wacce bata zoba daga inda ta ke, kuma ranan naga Yayah Auwal, domin ya ƙira video call don yaga takwaran shi, bawai ba'a taɓa mishi takwara bane, a'a yaji daɗin na wurin M.G sosai akace, domin shima gani yake yiwa M.G ɗane a wurin shi, babyn yana hannu na lokacin da M.G ya shigo da wayan, bayan sun gaisa da heedayah ne, M.G ya miƙo mun wayan yana cewa "Yayah ga matar A.G da takwaranka", kai so masha Allah, inaga duk ƴaƴan Goggo masu kyaune da farin fata, don ko yana xaune turai ne, duk da girma ya fara kama shi amma naga duk yafi su fari da kyaun, fuskan shi ɗauke da murmushi yana kallon fuskan babyn yace, "barka da ƙanwata, yyh Aminu yayah takwara na? Fatan yana cikin lafiya ko"? Sai da nasake ɗaga ido na dube shi, wai nan hausa yake yi, amma kaman turancin ne a bakin shi, ashe bayan M.G dana sani da mugun iya turanci ashe akwai wanda ya fishi a gidan su? Ko da yake duka ƴaƴan Goggo masu ilimine, don Yayah Sani yanzu professor ne, shima kuma yayah auwal ɗin hakane, twins kuma dukan su P.H.D suke da, Drs ne su duka, Yayah Rabiu ne kawai iya kaciɓ dhi degree ya kama ball, duk da nace kuma wai Yayah auwal ɗinne kawai ya fishi ƙwaƙwalwa, kawai dai nashi abincin a ƙwallo ne ba a boko ba, murmushi nayi na amsa mishi da komai lafiya.
Suna yayi kyau mun chakare abunmu, amma tun ranan sunan kuma zaman ƙafiya tsakani na da abinci ya ƙare, don tun da naji warin alale hankali na ya tashi, sai duk lokacin da zanci abinci sai naji warin a hanci ne, sai naji bazan iya ba, dole rayuwata ta koma daga tea, sai idan ka matsa nace zan sha garin kwaki.
Watarana naje gaida su Aunty B, don jikinta daya ɗan matsa, duk sai nakasa cin komai, da yayah muhammad ya matsa sai nace ni garin kwaki kawai nake so, jikin shi na rawa ya fita nemo mun, daya dawo kuma ya taho mun da gyaɗa da ƙarago wai ya tuna yadda suke sha da a school, hakan kuma ya mun daɗi, sai naji na daka ƙaragon na kwaɗa kawai, aiko na kwaɗa na zuba albasa da attarugu, daga ni har duka Aunties ɗina muka dinga ci, muna cine naji Aunty B tace, "Besty cikin ki how many months kenan"? Tsayawa nayi da cin nace, "ciki kuma Aunty? Ni ae Aunty banida ciki, tunda nayi miscarrige ae har yau ban sake period ba".
Dariya suka kwashe ita da Aunty j, "tazarce kenan kikayi"? Aunty j tace, nidai tsayawa nayi ina binsu da ido, a zuciyata kuma ina mamakin wai ina da ciki, tou wani irin cikine kuma babu ciwo babu komai?
Shigowan yayah muhammad yaga suna ta mun dariya ni kuma ina zare ido ya tambaye su da lafiya kuwa?
Nan Aunty B ta mishi bayani, shi dai murmushi yayo kawai yace , "ae sai suje asibiti ayi test ko?inaga hakan zaifi kwanciyar hankali", nidai shiri nayi ina tunanin in da gaske cikine wani irin farin ciki Jarumina zaiyi? Sai naji gaba ɗaya asibitin kawai nake so muje mu tabbatar, basu ankara da ni ba na ɗauki waya na tura mishi message.
Aikuwa ko ƙwaƙƙwaran awa uku bai cika ba ya baro abunda yakeyi ya taho gidan, mudai kawai ganin shi mukayi yazo, kuma yace na taso muje asibitin, dariya sosai Aunty B ta mana ta kuma mana fatan alkhairi, garin kwaki na ta ɗauko mun, karɓa nayi muka wuce.
Scarning Dr ya mun, inda ya juyo yana duban A.G.
*AUNTY NICE*