Yadda Za Ki Gyara Fuskar Ki Da Furen Tumfafiya Ta Yi Sheki Da Kyan Gaske

Yadda Za Ki Gyara Fuskar Ki Da Furen Tumfafiya Ta Yi Sheki Da Kyan Gaske

 

 

Kamar dai yadda kowa ya sani ana sarrafa Furen Tumfafiya ta ko wacce hanya, domin samun biyan buƙata musamman ga 'yan uwa mata, da ke son gyaran jiki. 

 
Na zo mu ku da hanya mafi sauƙi da zaki gyara fuskar ki cikin sauƙi ba tare da tsawwalawa ba, gare ki 'yar uwa.
 
Da farko zaki tana di Furen Tumfafiyarki daidai yadda ki ke so. Ki tanadi Cotton wato kaɗa a gefe.
 
Ki dinga goga Furen a fuskarki, wannan danshi danshin ruwa ake so. Ki saka kaɗa kina murza ruwan a fuskar. Idan kin tabbatar da ruwan sun mamaye ilahirin fuskarki, sai ki jira zuwa minti biyar sa'annan ki saka ruwan ɗumi ki wanke fuskarki. 
 
Ki gwada wannan na tsawon sati ɗaya Sister, za ki ga yanda fuskarki za ta yi sheki da kyau.