Gwamnatin taraiya ta tura dakarun kare dazuzzuka 7,000 don fatattakar ƴan ta'adda

Gwamnatin taraiya ta tura dakarun kare dazuzzuka 7,000 don fatattakar ƴan ta'adda

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara tura sabbin jami’an kare dazuzzuka (Forest Guards) sama da 7,000 zuwa jihohin Arewa bakwai, a wani babban yunƙuri na dawo da ikon gwamnati a dazuzzukan da suka zama maboyar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan ta’adda.

Jihohin da aka fara tura jami’an sun haɗa da Borno, Sokoto, Yobe, Adamawa, Niger, Kwara da Kebbi, inda aka ce wannan shi ne kashi na farko na shirin tarayya da ke haɗa yaƙi da ta’addanci da kuma kare muhalli a lokaci guda.

A yankunan karkara na Arewa, dazuzzuka sun dade suna zama tushen rayuwa da kuma barazana a lokaci guda  amma kuma ‘yanbindiga ke fakewa bayan hare-hare.

A Danko-Wasagu na jihar Kebbi, manoma sun bayyana farin cikinsu.

“’Yan bindiga sukan fito daga daji su kai hari cikin sauri, su kuma ɓace,” in ji Malam Yakubu, wani manomin masara. “Idan wadannan jami’ai sun fi sanin daji fiye da ‘yan bindiga, watakila za mu fara kwana da kwanciyar hankali a yanzu.

Shugabannin al’umma sun ce wannan mataki alama ce ta komawar gwamnati cikin yankunan da jama’a suka dade suna jin an yi watsi da su.

Muhimmin mataki a tsarin tsaro

A yayin bikin kaddamarwa a Abuja, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa:
“Wadannan Forest Guards ba kawai jami’ai masu sanye da kaya ba ne. Su ne masu kai ɗauki na farko, masu kare al’umma, kuma muhimmin ginshiƙi a tsarin tsaron Najeriya.”

An ce horon ya kasance mai tsauri, inda kashi 98.2% suka kammala horon cikin nasara. Sai dai jami’ai biyu sun rasu sakamakon matsalolin lafiya, yayin da aka kori 81 saboda rashin ladabi da karya ƙa’ida.
Gwamnati ta jaddada cewa an koyar da jami’an mutunta haƙƙin ɗan Adam da amfani da ƙarfi cikin hankali, domin kauce wa cin zarafin fararen hula.

Abin da ake tsammani daga gare su

Ribadu ya ce aikin Forest Guards ya wuce sintiri kawai:

Za su riƙe yankunan da gwamnati ta dade ba ta kai hannu ba.

Za su zama ido da kunnen hukumomin tsaro a dazuzzukan da suka zama marasa gani ga ƙasa.

Za su tattara bayanan sirri daga al’umma
Za su katse hanyoyin motsin ‘yanbindiga
Za su kare manoma da mazauna karkara.

Haka kuma za su yi aiki tare da sojoji da ‘yan sanda, su buɗe hanyoyin noma da titunan daji, tare da dakile hakkin ma’adinai da sare itatuwa ba bisa ƙa’ida ba.

“Ta hanyar kare dazuzzukanmu, zamu karɓo yankunan Najeriya,” in ji Ribadu. “Kuma da karɓo yankunan, muna kare rayukan ‘yan Najeriya da makomarsu.”

Daukar ma’aikata daga tushe

An bayyana cewa an ɗauki jami’an ne daga cikin al’ummomin yankunan, domin su fi sanin hanyoyin daji, koguna, ramuka da wuraren fakewa da ‘yan bindiga ke amfani da su.

Masana muhalli sun ce wannan shiri zai iya katse hanyoyin samun kuɗin ‘yan bindiga, musamman ta hanyar sare dazuzzuka da hakar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.