Yadda Za ki Sarrafa Ganyan Darbejiya Wajen Gyaran Fuska
Sheƙin fuska, ko kuwa laushi da yalwataccen haske marar algus ki ke buƙata?
Yadda zaki sarrafa ganyan darbejiya wajen gyaran fuska ta samu da ake bukata wanda kowa zai yi alfahari da kasancewar hakan.
Sheƙin fuska, ko kuwa laushi da yalwataccen haske marar algus ki ke buƙata? A wannan sinadarin da aka kawo maki zai yi tasiri a biyan bukatarki kuma za ki sam barka matukar ki ka gwada wannan al'amari mai cike da ban kaye.
Muje zuwa:
Za ki tanadi ganyen darbejiya wato ganyen iccen dogon yaro, ga Sakkwatawa ganye wanda ya ke kan tsiro ba wai wanda ya nuna akan iccen ba, sabon toho nake nufi.
Sa'annan a nemi Kurkum, ya danganta da colour ɗin da ki ke ra'ayi.
Sai ɗanyan ƙwai.
Za ki nemi turminki tsaftatatce ki fige ganyenki daga jikin ɗan iccen da aka ɗebo miki shi, ki daddakashi ya daddaku, ki tabbatar kinsa ruwa kaɗan ba da yawa ba. Sannan ki kwashe cikin mazubi mai kyau.
Ki nemo rariya ki tace wannan dakakken ganyen naki, saiki ɗauko kurkum ɗinki ki zuba a cikin wannan dakakken ganyen naki. Ki haɗesu waje ɗaya, sannan ki fasa kwanki ki kaɗeshi ya kaɗu, saiki zuba shi cikin haɗin ganyenki da kurkum ki game su wuri ɗaya, ki tabbatar kinyi haɗi mai kauri domin haɗin mai kaurin ne za ki shafa a fuskarki tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin saiki wanke da ruwan ɗumi.
Idan akwai ragowa zaki iya saka shi a cikin freezer bazai yi komai ba harya ƙare.
Duk macen da za ta gwada wannan a fukarta za ta sha mamakin yanda bukatarta ta biya tare da kashe wasu makudan kudade ba. Fuskar 'ya mace nada matukar daraja da yakamata a daina wasa da ita wurin gyanta da ingantata domin kusan ita ce kwalliyar 'ya mace.
DOCTOR MARYAMAH.