Mata: Tsakanin Sakaci da Soyayyar  Iyaye a Ina  ake Samun Lalacewar Tarbiya 

Mata: Tsakanin Sakaci da Soyayyar  Iyaye a Ina  ake Samun Lalacewar Tarbiya 

 

Duba da yanda tarbiyar 'ya'ya mata ke Kara tabarbarewa ya janyo hankalin mutane kan menene sanadin haka?

 Tabbas akasarin 'ya'ya mata da suka lalace ya samo asali ne daga sakacin iyayen mu mata. 

Uwa ita ce wadda take bayar da tarbiya ga 'ya'ya Kuma ita ce babban madubi ga 'ya'yanta. Amman saboda sakaci da Kuma nuna rashin son ganin laifin yaranmu ya Sanya ko mun ga yaranmu sun bi halin da bai da ce ba sai muyi halin ko oho saboda ba mu son ganin bacin ran su. Za ka ga yarinya tace ma mahaifiyar ta za ta je gidan abokiya, ke uwa baki san wacece qawar ba, wace irin tarbiya qawar take da shi? Daga nan gidan qawa ina za su je? Me suke kullawa ita da qawar? Su waye iyayen qawar?  Wadannan su ne tambayoyin daya kamata ki yi ma kanki kafin ki saki 'yar ki taje gidan qawa. 

Na biyu Kuma shi ne: irin dunkunan da muke wa yaranmu mata da sunan kwalliya. 
Uwa kin dauki kayan sallah yaran ki kin kai wurin dinki, Kuma ke ce kike tambayan a baki styles na zamani saboda kina son yar ki ta fito. Shin kin manta cewa ke ce Mai bayar da tarbiya, kin manta Shigar tsiraici kan janyo fyade ga 'ya'yanmu mata? Burin ki kawai shi ne 'yar ki ta fito tafi kowa kyau. 
Na uku: mene ne alfanun wayar zamani ga yaranmu mata? Especially under age.

wayan zamani tana da amfani sannan tana da nata rashin amfanin, Kuma yaran mu ba su da wayon banbance Hakan. Kin dauki waya kin ba yarinya, ta shiga daki da waye take waya? Da waye take charting? Wani website take shiga? Duk bamu damu ba saboda soyayya. Yakamata mu iyaye mata mu canza, mu Kula sosai da tarbiyan yaranmu domin samun Al'umma ingantacciya. Allah ya tsare muna zur'ianmu ya ba mu ikon ba su tarbiya. 

Daga Safiya Usman