Wannan shi ne tsarin da mace za tayi sallah bayan ta samu tsarki.
1:- Idan mace ta samu tsarki kafin bullowar Alfijir. Za ta sallaci magariba da isha'i sannan ta yi Sallar asuba.
2:- Idan ta samu tsarki bayan bullowar Alfijir kafin fitowar rana. Zata sallaci asuba ne kawai.
3:- Idan ta samu tsarki bayan bullowar rana to ba zata sallaci asuba ba sai dai ta
fuskanci azahar.
4:- Idan ta samu tsarki bayan Sallar azahar kafin sallar la'asar zata sallaci azahar ne kawai.
5:- Idan ta samu tsarki bayan la'asar to zata sallaci azahar da la'asar.
6:- Idan ta samu tsarki bayan magariba kafin isha'i zata sallaci magarba kawai.
7:- Idan ta samu tsarki bayan isha'i zata sallaci magarba da isha'i.
A sanar da mata wannan a kuma yada sakon saboda muhimmancinsa. Allah ne mafi sani.
Allah yasa mudace yataimake mu duniya da lahira