Dandalin Cigaban  Sakkwato ya kara wa'adin shugabaninsa don daurewar kungiyar

Dandalin Cigaban  Sakkwato ya kara wa'adin shugabaninsa don daurewar kungiyar

 

 

Dandalin cigaban Sakkwato waton SOKOTO ADVANCEMENT FORUM(SAF)  da aka samar domin kawo cigaba da kula da yanayin al'ada da mutuncin jiha ya kara wa'adin jagorancin shugabaninsa har zawa bayan kammala zaben 2027 yana ganin hakan ne kawai  zai kawo daurewar kungiyar.

Shugabanin dandalin ne suka yanke shawarar a babban taron da suka gudanar a dakin taro na kwalejin Ummaru Ali Shinkafi dake Sakkwato a satin da ya gabata.

Mambobi gaba daya sun goyi baya, domin suna ganin in ba a yi hakan ba siyasa na iya yi masu barazana a gudanar da dandali.

Shugaban dandalin Ambasada kuma Farfesa Muhammad Ahmad Wali a jawabinsa wurin taron ya ce an samar da dandalin ne domin ganin an cika burin gwamnati ga samar da cigaba da abubuwan more rayuwa don tabbatar da cigaba mai dorewa a jjiha.

Farfesa ya ce jihar na fama da matsalolin tsaro da ilmi da lafiya da komawa baya, kan haka suke ganin dacewar a hada kai tsakanin mutanen jiha da gwamnati don shawo kan matsalolin da suka addabi jihar.

Ambasada Wali ya yabawa shugabanni da mambobin dandalin kan sadaukar da kansu ga kawo cigaba ga al'ummarsu ta jiha, ya bukace su da su kara aiki tukuru don ganin burin dandalin ya cika a haujin ilmi da kiyon lafiya da tsaro.

Daya daga cikin mambobin kungiyar Dakta Nafisa Adumu Gurori ta jawo hankalin shugabanin na tsayawa a yi aiki don Allah da kuma jajircewa kar a bari dandalin ya mutu kamar yadda wasu kungiyoyi a jiha suka yi, sun taso ana murna zuwa wani lokaci ka neme su ka rasa.

Gurori ta yabawa shugabannin da suka fito da wannan tunani ta yi fatar cika burinsu, ganin dukan shugabannin mutane ne da a jihar Sakkwato ake gani da mutunci da kima.

Daya daga cikin mahalarta ya kalubalanci shugabannin kungiyar da su samo bakin zaren da ya sanya Sakkwato ta zama mafi talauci a Nijeriya sabanin Kebbi da Zamfara da Neja da aka fitar cikin jihar.

Mataimakin shugaban dandalin Farfesa Arabu Shehu ya karanta daftarin dokokin kungiyar domin amincewa da  gyara.

Farfesa Shehu ya roki mahalarta da su mayar da hankali a harkokin dandalin hakan zai karawa shugabanni kaimi da zaburarwa a kan abin da aka sanya gaba na kawo cigaba a jihar Sakkwato,

Dandalin shi ne mafi karfi da ya tara manyan 'yan boko a jihar, da  suke iya sauya jiha daga ci baya zuwa cigaba matukar suka samu hadin kai a tsakanin mambobinsu.