APC DA PDP: Kotun Daukaka Kara Za Ta Fara Sauraren Shari'ar Sokoto A Abuja

Haka ma jam'iyar APC a jiha ta daukaka kara a cikin hukuncin da aka yanke a Tarabunal da ya shafi maganar takardun makaranta, in da a gefensu hukuncin da aka yanke nada gyara a ciki duk da ba masu Kara aka baiwa nasara ba.

APC DA PDP: Kotun Daukaka Kara Za Ta Fara Sauraren Shari'ar Sokoto A Abuja

Kotun Daukaka Kara dake zama a Abuja ta Sanya ranar Talata domin soma sauraren Shari'ar da jam'iyar PDP ta Sanya a gabanta in da take kalubalantar hukuncin Tarabunal wadda ta tabbatar da nasarar jam'iyar APC da Gwamna Ahmad Aliyu Sokoto a zaben da ya gabata.
PDP da Dan takararta Malam Sa'idu Umar ba su gamsu da hukuncin ba hakan ya sa suka tafi kotu ta gaba domin sake duba hujjojinsu da suka gabatar.
Haka ma jam'iyar APC a jiha ta daukaka kara a cikin hukuncin da aka yanke a Tarabunal da ya shafi maganar takardun makaranta, in da a gefensu hukuncin da aka yanke nada gyara a ciki duk da ba masu Kara aka baiwa nasara ba.
Lauyoyin bangaren guda biyu PDP da APC sun shirya tsaf domin gafartawa a gaban Alkalan kotun Daukaka Kara in da za a raba zare da abawa.