Yadda Za Ki Gyara Fuskarki Da Sukari Ta Yi Kyau Sosai

Kina son ki zamo tauraruwa a cikin mata?  Kina son ainihin hasken fuskarki ya fito gwanin sha'awa?

Yadda Za Ki Gyara Fuskarki Da Sukari Ta Yi Kyau Sosai
Daga Dakta Maryama

Kina son duk inda ki ka shiga ki dinga ƙyalli tamkar daren goma sha tara? 
Kina son ki zamo tauraruwa a cikin mata?
 Kina son ainihin hasken fuskarki ya fito gwanin sha'awa?
'Yar uwa nesa ce ta zo kusa, domin kuwa cikin sauƙi zaki iya gyaran fuskarki ta zamto miki gwanin sha'awa.

Za ki sami Sugar ki daidai misali, ki kwaɓata da ruwa dallah dallah. Sannan ki shafa ta a fuskarki, kin murza daidai misali ta yadda wannan 'ya'yan sugar ɗin za su samu damar narkewa kan fuskarki. Idan kin tabbatar sun narke sai ki bar sugar ɗin a fuskarki kimanin 30minutes, sai ki sami ruwan ɗumi ki wanke fuskar da su. 
Hummmm! Ba'a cewa komai, domin kuwa sai an gwada akan san na ƙwarai in ji masu hikamar zance.