Ƙalubalen Gyaran Jikin Mata A Lokacin Damana
*Damana*
Lokacin damina na kawo canje-canje sosai a muhalli da yanayin jiki musamman ga mata. Danshi da sanyi na kawo kalubale wajen kula da lafiyar fata da tsabtace jiki, wanda ka iya haifar da cututtuka da ka haddasa rashin kwanciyar hankali da rashin jin daɗin jiki.
1. *Ƙalubalen Ta Fuskar Gyaran Jiki*
- *Danshi da rashin bushewa:*
Yana kawo ƙaiƙayi da warin jiki da ƙuraje na musamman ga ma'abota yawan shiga kwantancin ruwan da suka gurɓace.
- *Matsalolin fata:*
Matsalolin fata suna ƙaruwa a wannan yanayin saboda ƙaruwar danshi. Matsalolin da aka saba fuskanta sun hada da cututtukan fungal kamar ringworm da athlete's foot, tashin eczema, fashewar ƙuraje, da ƙurajen fata. Waɗannan matsalolin sau da yawa suna ƙara ta'azzara ta hanyar ƙamammen gumi, maiƙo da datti, wanda ke haifar da toshewar ramukan fata da kuma yiwuwar girman ƙwayoyin cuta ko fungal.
Lokacin damina akasarin mutane musamman ƙananan yara suna fama da matsalar ƙurajen fata, fashewar fata da kumburi.
- *Faɗuwar gashi da amosanin kai (dandruff):*
Yawan jiƙewar gashi da rashin bushewa musamman ga mata masu ɗabi'ar wasa a ruwa (Shil-lalo) wanda hakan kan iya haifar da amosanin kai.
- *Ciwon farji (vaginal infections):*
a kan iya samun wannan matsalar a lokacin Damana sakamakon amfani da jiƙaƙen ɗan kamfai ko sanya mai danshi, datti ko ma saka jiƙaƙƙin tufafi.
- *Warin ƙafa da fashewarta*
Ana iya samun wannan matsalar idan aka yawaita tafiya cikin ruwa ba takalmi da kuma rashin samun isasshen iska a ƙafafu.
*2. Illolin Da Ke Tattare da Hakan*
* Yaɗuwar cututtuka na fata da al’aura.
* Wari da rashin kwanciyar hankali.
* Yawan shan magani da rauni ga lafiyar mace.
*3. Matakan Kariya*
° Yin amfani da ɗan kamfai (pant) mai auduga wanda ka iya taimakawa wurin busar da jiki sosai.
° Gujewa takalma masu rufe mashigar iska a ƙafafu.
° Shafa mayukan gyaran fata
° Tsaftace al’aura da kyau tare da matsugunni.
° Ziyartar likita idan akwai alamar wata matsala daga cikin waɗannan ko mai kama da ita.
*Manazarta*
Healthline. (2023). *Fungal infections in humid weather*. https://www.healthline.com
Mayo Clinic. (2021). *Skin care tips during rainy seasons*. https://www.mayoclinic.org
Medical News Today. (2023). *Causes and prevention of vaginal yeast infections*. https://www.medicalnewstoday.com
National Institutes of Health. (2020). *Women’s health and seasonal hygiene*. https://www.nih.gov
World Health Organization. (2022). *Personal hygiene in wet seasons*. https://www.who.int
managarciya