Mi Ya Hana Gwamnatin Sakkwato Taya Sarkin Musulmi Murna?

Mi Ya Hana Gwamnatin Sakkwato Taya Sarkin Musulmi Murna?

Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar ya cika shekara 17 saman karagar sarautar gidan Danfodiyo.
An al'adanci gwamnatin jihar Sakkwato takan Sanya talla a jaridar turanci ta Daily Trust a ranar da shekara ta zagayo na hawa kan karagar, sai dai a wannan shekara gwamnatin Sakkwato ba ta Sanya taya murnar ba, abin da mutane ke tambayar dalilin haka don sanin inda gizo ke saka.
Mutane sun yi tsammanin a saka taya murnar saboda gwamnatin sabuwa ce wannan bukin ne karon farko da Sarkin Musulmi ya yi karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto, sai gashi an samu akasin hakan ba a yi ba.
Sanya murnar nada tasiri ga mutanen jiha da masarauta gaba daya don Wani abu ne na  nuna taren juna da hadin Kai Wanda ake bukata a cikin tafiyar da gwamnatin siyasa da masarauta.
Yakamata gwamnati ta rika daukar irin wadannan hidimar da muhimmanci don hakan zai kara Sanya karsashi ga masarauta.
Mutane na ganin dalilin gwamnati na kin saka taya murna Wani abu ne da ya shafi gwamnati. Ko mine ne dalilin dai taya murnar nada nasa muhimmanci a tafiyar jagororin na jiha.