Bankuna za su fara cajin harajin ₦50 daga 1 ga watan Janairu

Bankuna za su fara cajin harajin ₦50 daga 1 ga watan Janairu

Bankuna za su fara cajin harajin ₦50 daga 1 ga watan Janairu

Bankunan Najeriya za su fara cajin harajin tura kuɗi na ₦50 kan duk wani kuɗi aka tura  da ya kai ₦10,000 ko sama da haka daga ranar 1 ga Janairu, 2026, bisa aiwatar da sabuwar dokar haraji.

Bankuna irin su UBA da Access Bank sun sanar da kwastomominsu cewa cajin, wanda ake kira Electronic Money Transfer Levy (EMTL), yanzu za a rika kiran sa harajin stamp, kuma mai aikawa ne zai ɗauki nauyin cajin, ba mai karɓa ba kamar yadda aka saba a baya.

An bayyana cewa tura kuɗi ƙasa da ₦10,000, biyan albashi, da tura kuɗi tsakanin asusu a banki ɗaya babu su a tsarin cajin. 

Bankuna sun ce cajin ya bambanta da tsarin harajin tura kuɗi na yau da kullum kuma za a bayyana shi a sarari a lokacin mu’amala.

A halin da ake ciki, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jaddada cewa sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, kamar yadda aka tsara, yana mai cewa gyaran na da nufin ƙarfafa tsarin kuɗi da sauƙaƙa bin doka ga ’yan kasa da ’yan kasuwa.