Halin da mata suka samu kansu Kashi 50 a lalacewar tarbiyarsu daga iyaye ne
Amma ya kamata uwaye su sani cewa,ba fa su kaɗai ne ke da hakki akan 'ya'yansu ba, su ma 'ya'yan nada cikakken haki akansu, duba da yadda annabi yace acikin hadisi cewa "KULLUKUM RA'IN, WA KULLUKUM MAS'ULUN AN RA'IYATAHI"

Halin da mata suka samu kansu Kashi 50 a lalacewar tarbiyarsu daga iyaye ne
A cikin kashi dari na rayuwar 'ya mace, kashi 50 yana lalacewa da taimakon iyaye.
Da yawan 'ya'ya mata rayuwar su ta shiga cikin garari a kan sakacin iyaye da suke yi a kan su, kafin da kuma bayan wata kaddara ta farma 'ya'yan na su.
Wannann rubutaccen sakon,ina son inyi amfani da shi wajen fadakarwa da tunatarwa ga iyaye maza da mata.
Iyaye su ne masu darajara ta uku a doron duniya,su ne mafi girman daraja ga rayuwarmu bayan Allah da manzon Sa, soyayyaar da ke tsakanin iyaye da 'ya'yansu, wata abu ce mai karfi,wadda ba wani mahalukin da za ka wa irinta, su ma haka din, son da iyayenmu ke mana ba yada kwatankwaci.
'Ya mace na fuskantar barazanar wofantarwa daga iyaye a duk lokacin da wata jarabta ta auku gare ta,wanda hakan shi ne mafarin lamarin tabarbarewar tarbiyarta.
Tabbas iyaye na kokarinsu a kan iyalinsu, saboda ko wace uwa ko uba, suna son yaransu su kasance yaran kirki, irin yaran da za'a bada misali da su acikin unguwa,a siffantasu da yaran kirki. Haka kuma ba uban da yake son ya haifi 'ya'ya ''yan iska wadanda za'a rinka Allah wadaran halayen su cikin unguwa.
Wasu iyaye na kokarin ganin sun gina rayuwar 'ya'yansu bisa turba da tsari na addini,tare da kafasu akan al'adu wadanda ba su ci karo da tarbiyar addini ba,wasu kuma sunyi watsi da hakan a mua'amalar su da iyalan su. Yayin da za ka ga wasu uwaye sun yi dai-dai da rayuwar iyalin su,ta yadda zaka ga wadannan ahali kamar wata bakuwar halitta ce.
Tabbas an san tarbiya daban shiriya daban!
Amma ya kamata uwaye su sani cewa,ba fa su kaɗai ne ke da hakki akan 'ya'yansu ba, su ma 'ya'yan nada cikakken haki akansu, duba da yadda annabi yace acikin hadisi cewa "KULLUKUM RA'IN, WA KULLUKUM MAS'ULUN AN RA'IYATAHI"
Ma'ana "dukan ku makiyaya ne,kuma za'a tambaye ku akan kiyon da aka baku."
Kuma acikin alqur'ani Allah ya na cewa "Ku anfusakum wa halikum naran,wa kudu hannasu wal hijaratu alaiha mala'ikatun gilazun shidadun." Har zuwa karshen ayar,
Wadda ita wannan ayar kai tsaye tana nuna cewa ba fa kai kadai zaka tserar da kanka daga wuta har da yalinka.
Mata masu kananun shekaru,sun fantsama cikin rayuwar kunci a kan iyayen su,
Jarabta za ta iya saukowa kowa,ba wani mutum da yafi karfin Allah ya jarabce shi da kowa ce irin kaddara. Kuma duk yadda iyaye na kai ga tarbiya ba zai hana wannan kaddarar ta fada kan 'ya'ya su ba, madamar Allah ya so da hakan.
Akwai mata da yawa wadanda suka zama rikakkin karuwai wadanda iyayensu su ne suka fi kowa laifi acikin wannnan tafiyar
Yarinya takan hadu da jarabtar cikin banza, maimakon ace iyaye su jata a jiki,su nuna ma ta muni da aibun wannan danyen aiki,da kuma illar sa ga addini da kuma al'adu, a'a ba haka za su yi ba,kokarin korata za su yi ga duniya,tare da sabon katin yarjewa akan wannan hanya,su na son ta je gaba ta kara gogewa,ta zam cikakkiyar 'yar iska.
Wai wannan shi ne tsololuwar horon da za su aikata gare ta,wanda sam ba wata tsoratarwa da yarinyar za ta ji,kuma zuciyarta zata kekashe,idanunta za su bushe,tsana zata karu acikin zuciyarta ta mutane,kullum tunanin ta,bata da sauran zama wata 'ya mai cikakken 'yanci,ko kuma zata dauki kanta wata halitta marar mamora cikin al'ummarta.
Minene alfanun korar da agabanka musamman diya mace,akan wani laifi da ta aikata,wanda kuma bata da wata hanyar da zata bi don ta goge kaddarar dake bayanta, tunda bata san kebantaccen ilimi na gaibu ba.
Hakan me ya ke nufi?
Fushi da ubangiji ko me?
Shin ubangiji bai isa yayi duk abinda ya ga dama ga bayin sa ba?
Ku iyaye don kun kori 'ya'yanku shi zai sa ku huce takaicin da kuke shaka sanadiyar wannan 'ya macen?
Ni dai ina ganin wannna magana bata nufin komai,sai son nunawa Allah me nayi masa ya jarabce ni da wannan fitinar. Ko kuma fito-na fito ga ubangiji, tare da zanga-zangar dole sai cire mummunan kaddara acikin ahalinmu.
Iyaye ba ku isa ku sauyawa Allah duk wani tsari akan bayinsa,don haka mafita daya ce,idan har an jarabce iyalinmu ta kowane fuska,kora da wasu maganganu da muke musu,ma su kama da tsinuwa,ko kuma kiran Allah ya halakar da wance, addu'a tafi komai muhimmanci ga rayuwarmu,kuma an san albarkar iyaye ta shallake duk wata addu'a. Ya kamata wadannan yaran ajawo su ajiki a nuna musu kauna da soyayya tare da munin wannan rayuwar da suka jefa kawunan su aciki.
Ba'a kori mace ba,korar bata haifar da komai sai karin tabarbarewa tarbiya.
Dafatar iyaye za su fahimci wannan.
Allah ya sa mu dace,Allah ya bamu ikon cin dukkan wata jarabta.
Nagode
Zainab Aliyu Sifawa.