Kwalliya: Shin Ko Kinsan Amfanin Da Madara Ke Yi Wajen Gyaran Fuska?

Idan ma baki sa ni ba,biyoni ki kwashi na ki rabon.

Kwalliya: Shin Ko Kinsan Amfanin Da Madara Ke Yi Wajen Gyaran Fuska?
 
Duba da yanayin sanyi da muke ciki, za ki iya sarrafa madararki domin ganin kin gyara fuskarki 'yar uwa.
 
 
Za ki sami madararki ta ruwa kowacce iri ce, peak  ko kuma threecrown ko Lahda ko Luna ko Nunu ce, duk wadda  ki ke da'ita dai.
Sa'annan ki nemo ayabarki mai kyau, ki nemo mazubi ki zuba madararki kimanin yadda ki ke ra'ayi.
Sai ki ɗauko ayabarki ki gyara ta, sai ki jefa ta a cikin ruwan madararki, ki saka hannu ki haɗe su wuri ɗaya, ki tabbatar haɗin ya yi kauri sosai.
Daga nan  ki dinga shafawa a fuskarki tsawon minti goma ko sha biyar kamin ki shiga wanka.
Za ki samu ruwa masu ɗanɗumi ba da yawa ba saiki wanke fuskarki da su. Tabbas 'yar uwa ina mai sanar da ke cikin ƙanƙanin lokaci za kiga fuskarki tana walwali ga sulɓi bugu da ƙari ga haske mai sanyaya zuciya.
Daga Alƙalamin Maryam