ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 54

ANA BARIN HALAL...:Fita Ta 54
Page 54
"Congratulation barr, madan na ɗauke da ciki na kusan 8weeks",  fuskan Dr cike da murmushi, ɗaga hannu sama A.G yayi yana hamdalah wa ubangiji, nidai na sunkuyar da kaina ƙasa ina wasa da yatsu na,a hankali ya saka nashi hannun ya riƙo nawa, ido na ɗago na zuba mishi, idan banyi ƙaryah ba hawaye ne cike a idon shi, baiyi magana ba amma alama ya nuna mun da ido, na tashi muje, miƙewa nayi hannu na cikin na shi, sallama sukayi da Dr bayan ya bu wani paper da zamu sayi  magani.
Har muka je pharmacy muka saya muka kama hanyar gidan mu baiyi magana ba, daga baya kuma dainaga ya juyo ya dube ni,   "ko akwai wani abu da kike so kici"?  Lumshe ido nayi na buɗe ina duban shi,   "ina son cin kwakwa da soyayyan kifi", mirmushi yayi ya juya hanyar winti market,  aiko leda guda aka ciko da kwakwa, kifi ma lodi guda aka sayo, kusan kala huɗu, sit ɗin baya ya ajiye ya dawo Sit ɗinshi ya zauna,  "sai kuma me beauty na? Me unborn ke so? Me cwit heart ɗina take so?" yana faɗa hannun shi akan lafaffen cikina yana shafawa, turo baki nayi gaba nace,  "boy ɗina dai, wacce irin takeso kuma, ni baby boy ne aciki?  Buɗe idon shi yayi duka a kaina yana murmushi,  "beauty insha Allahu girl ce, kin san yadda nake son yara mata kuwa? Duka girls zaki bani insha Allahu, ke ko ɗaya sai nayi ƙoƙarin baki tunda kina so",  tada motan yayi muka kama hanyam gida, still hannun shi ɗaya yana riƙe da ni.
A parlon shi mukayi masauƙi, shi ya ɗauko ledojin, direct kitchen yaje ya jubge mun so, bai fito ba sai da ya ɓare mun kwakwa guda, ruwan ya juye mun a wani ƙaramin cup, kifin kuma ko wanne a ciki sai daya saka mun akan filet, inda nake yazo ya ajiye mun,  idona akan shi ina jin wani azababben son shi yana ratsani,  murmushi ya mun ya ajiye komai akan stool ya matsu mun da shi a gabana,  kifin kuwa na dirawa, ko wanne sai dana ɗauki ɗaya aciki na taɓa, a ƙarshe na tsaya akan wani buɗaɗɗe kaman banƙararren kaza, shi sai danaci har biyu, bayan wanda naci a farko, tissue ya miƙo mun ma goge hannu na da baki na, sannan na ɗauki ruwan kwakwan nasha, hannu na ɗauka na ɗauko kwakwan, ina sakawa bakina na wani runtse ido tsabar daɗin da ya ratsa ƙwaƙwalwa na,  murmushi yayi yana bina da kallo,  "Eeshaa na baza a ɗan samma A.Gn Eesha bane"?  
Kallon shi nake ina murmushi,  "Jarumina ae kaine baka nemi zaman lafiya ba",  na faɗa ina murguɗa bakina,  murmushin shi ya faɗaɗa,  "beauty me nayi kuma"?  
"Kace baby girl ne, ni kuma boy nakeso don mu saka sunan M.G" na faɗa ina kallon shi ido cikin ido.
Dariya yayi ya tashi daga tsugunen da yake a gabana, gefen inda nake zaune ya zauna " beauty ina fatan Allah ya raya abinda ke cikin ki, idan tazo duniya sunanta *KHADIJAH* sunan ummie zan saka saboda ta bani farin cikin rayuwata, ita ta haifa mun beauty nah, ita ta bani kyauta mai girma da daraja a rayuwa na, ina so na faranta mata yadda ta faranta mun, ina son na girmamata sama da wanda ta haifi mai mun,
Na biyu kuma zan daka Heedayah, ina son ta sosai, ina ƙaunar ta, gashi kuma tana riƙe mun da farin cikin rayuwata, M.G, tunda aka haifi heedayah nake jinta kaman zuciyata, amma in kin cire M.G da mummy kowa gani yake Hudah ce tawa, ita nutsuwanta yake samu zama inuwa ɗaya  Heedayah kuma hattah sunanta ni ma zaɓa mata shi,ni nayi kusan rabin rainonta, shi yasa naji daɗin aurenta da M.G.
Na ukun sai ki haifi naki boy ɗin, na huɗu kuma girl nake so, ita kuma RASHIDAT, (mummy) ce, auta ta da zan mata kauna na daban, ƙaunar da babu wani mahaifi daya taɓa yiwa ɗiyar shi irin shi, zan so ta sama da irin son da mummy tayi mun, xan so yarah na sosai beauty",  ya faɗa yana kwantar da kanshi a kafaɗa na, ajiyan xuciya na sauƙe,  "kaɗa fah ka so su sama dani",  na faɗa ina kai mishi kwakwan bakin shi, murmushi yayi ya gutsuri kwakwan sannan yace,  "hmmm beauty kenan, ni ae babu wani abu da zai zo yafi mun ke a rayuwan nan, bana fatan ganin hakan ma, amma dai kada fah ki fara kishi da su axo ana ƙin basu nono su sha, don zamu samu matsalah akansu fah ƴan mata na",  dakata wa nayi da cin kwakwan na ɗaga anshi na ƙura mishi ido,   "bangane magananka ba jarumi nah? Kana nufin akan su zanga ɓacin ranka? Kenan ma ka zaɓe su sama dani"?  Na faɗa bakina a ture a gaba.
Rungumeni yayi yana dariya, sanann ya chanja topic ɗin,  "Beauty next week zanje lagos, kuma inaga zamuyi 1week nida barrister, zamuje ko"?  Tashi nayi nayi hanyan ɗakina don nayi wanka, kallon shi nayi ban ce uffan ba, shidai dariya kawai yake mun,don yasan na shaƙa ne game da maganan zaiso yaran shi da yawa, kaman ma sama da ni.
Cikina yana six month lokacin Aunty j ta haihu, wannan karon ma ɗa namiji, ta haifah, gashi kowani yaro kama yake da gidan mu, yaran nan babu abunda suka baro na yayah Ahmad, a lokacin kuma aka saka Date ɗin auren mutane na, Yayah umar da ummitah, yayah ishaq da hafsyn shi, gashi garin zaman su ya banbanta, shi yayah umar kaduna yake, yayah ishaq kuma Maiduguri, (october 2023) bikinsu, ni kuma zai kama na haihu da kusan 6month kenan,an saka date ɗin da nisa saboda zasu tafi wani training ne na six month, shi yasa aka kai shi wannan lokacin.
A cikin wannan watan da zamu shiga ne bikin hadiza, saboda haka nayi shiri sosai na zuwa bauchi, bamu samu zuwa a lokacin da muka so ba, sai ranan friday ɗin bikin muka tafi, don ma flight ɗinmu na safene, tafi da gidanka mukayi, don gaskiya duk yayuna sunyi kara, mun iso wuraren 10:00am, gida naso wucewa amma fir A.G yaƙi amincewa, amma ganin Heedayah ma gidanta zata sauƙa sai abun ya ɗan mun sauƙi, gidan su muka wuce nida shi da M.G da kuma heedayah, inda su Aunty B ma da mazajen su da yaran su gidan mu suka shige, achan mukayi break, bayan munyi na matsawa A.G akan zanbi su Aunty B zuwa garinmu, inda achan zatayi event ɗinta.
Saida mukaje gidanmu ya ɗan gwangwaje ni yadda yaso tukun muka ƙarisa sir kashim, ina shiga kuwa nayi karo da ummie na ta fito daga ɗakinta xatayi kitchen, aiko banji nauyin cikina ba, banji kunyan su yayah da dukkansu suna parlon ba naje na rungumeta, murmushi cike a fuskanta tana kallon na cike da tausayawa irin na uwa idan taga ƴarta ɗauke da ciki, gashi kowa yayi mamakin bajewan dana ɗanyi, babu wanda yayi tunanin zanyi jiki haka, duk da dai ƙarfin cikin a cinyoyina ne, amma kuma shima ya ɗan tasa kaɗan.
Muna rungume da juna Su Aunty suna mun dariya, hafsy ka sai mita takeyi wai zan kayar mata da mahaifiya na fallashe ta, nidai ban bar jikin ummie ba ina ta murmushi ido na cike da ƙwallan daɗin ganina tare da ita, a haka A.G ya shigo parlon, ganin shine ma yasa ummien ɗan matsar dani a jikinta, dawowa tayi cikin parlon sosai ta zauna tana amsa gaisuwan shi, hira akan ɗanyi a parlon kaɗan, sannan yayah muhammad yace mutashi mu tafi kafin a fara shirin jumma'a , haka ko akayi, mota ɗaya aka ce zamu yi tafiyan da ita.
hajiya ummah ance tayi sati achan, tafiyan da mamah zamuyi, sai Aunty B, Aunty J, ni sai Hafsy kuma, mamie da ummie ance gobe zasu taho da su yayah ƴan ɗaurin aure, fitowan mu dukkan mu muka wuce side ɗin mamie don a gaisheta, nidai ina ta bayan yayah muhammad, kuda muka shiga muka samu Raliya da mamie zaune a parlor suna cin abinci suna hiran su ƙasa-ƙasa, ban fito fili yadda zata ganni sosai ba, gaisheta mukayi tana wani bin mu da kallo kaman taga kashi a zube a wurin, yayah Ahmad ne ke tambayan Raliya dama tazo ne? 
Kafin ta bashi amsa mamie tayi charaf tace,  "taxo tun ranan laraba, ina xaku sani kun watsar da ita kaman ita ba ɗaya take da su Ayshaa ba a wurinku, tou ina zaku sani tunda ita ta dawo bare a cikinku,
Ta faɗa tana wani banzan kallo wasu Aunty B da suke miƙewa domin barin parlon, shi ma A.G miƙewa yayi yabi bayan su, nidai ina manne sosai ta bayan yayah muhammad, don ni ko cikin bana so ta gani, don ma ummie ne tace na biyu su mu shigo tare amma da banyi niyyan zuwa ba.
Murmushi yayah muhammad yayi sannan yace,  "mamie kenan Allah ya rufa asiri, amma ita inaga ko number ɗaya daga cikin mu bata da shi, ba'a taɓa mana haihuwa ta ƙira wani tayi barka ba ballantana taje suna, ina kaduna ina Abujah"?
Sunkuyar da kai ƙasa Raliya tayi alaman ta ɗan ji kunya, don yaushe ma su yayah muhammad suke magana ballantana har du nuna maka abunda kayi ya ɓata musu rai ko baiyi daɗi ba a wurin su?
"Tou ae ganu tayi baku damu da ita bane, waye a cikin ku ya taɓa bin inda take? Don kunga ita Allah bai bata haihuwa ba ko? Don ma yanzunaga alaman sun zama biyu, don ga ita Ayshann ma abokiyar auren ta har ta haihu amma ita shiru, anyi biyu kenan a gidan magadan mamah, Allah dai yasa ba maman suka gado ba".
Miƙewa mukayi dukkan mu, yayah Ahmad ne ya bata amsa da,  "insha Allahu suma zasu haifi nasu, fatan da muke musu kenan",  ni dai fit nayi na fice a parlon,  gaban motan na shige na xauna, inda mamah da Aunty B suka zauna a tsakiya, chan baya kuma Aunty J da hafsy suka zauna, yara kuma dama Aunty j ta ajiye su a gidan su, daga Areefh har Ameer ɗinta, babynta Ammar kuma yana riƙe a hannun Yayah Ahmad, sai da ta shiga tukun ya miƙa mata shi, addu'a sosai suka mana, A.G dai babu ko kunya yana tsaye a ƙofan da nake zaune, sai da driver zai tashi ya ɗan sunkuyo kaɗan yace,  "ki kula mun da baby nah plz beauty",  murmushi nayi na mishi alaman ummie fah naganin mu, itama ummin kaman tasan magananta nakeyi sai ta juya ciki, lumshe mun ido yayi bayan ya kashe ido mun ido ɗaya, murmushi nayi na ɗagawa su yayah hannu, da fatan sai sun shigo goben idan Allah ya kaimu.
Hadiza taji daɗin zuwan mu sosai, achan muka samu zainab da maryam besty nah, aiko munsha chaftah ranan, suna ta zolayana da cikin A.G, maryam har da cewa,  "yanzu yadda A.G yake wani ciccin magani yana basarwa haka ya juye wa ƴar mutane ciki babu kunya"?  Dariya da kan mu mukayi, bakina baiyi shiru ba nace,  "yadda Dr Abduol babu kunya ya juye miki nashi haka shima Jarumi na ya juye mun nashi",   na faɗa ina juya ido ina rausayarwa, dariya duka mukayi  Anan kuma aka ƙira fatima itama aka zolayeta, sannan aka ƙira jammy aka sha dariya da ita  don video call akayi da su dukkan su, haka kuma sukayita zolayana, Allah sarki ƙarshe sai da nafara kukan tunawa da sisto na habiba, kai rayuwa ina jin mutuwan habiba kaman zai fasa mun zuciya idan na tuna, habiba tana son taji ana labarin rayuwar aure tsakanin mata da miji, ana farawa zakaga ta matso tana munafukin dariya, gashi yau babu ita a duniyan, kukan da nafara ne ya kawo ƙarshen rahan mu,  dayake a side ɗin matar yayanmu babban wan su hadiza muka zauna, ɗakuna biyu ne sai muka kama ɗaya,  haka duk jikin kowa yayi sanyi,ita dai zainab tashi tayi ta fice dama tun wuri, ita zainab bikinta da Abdoulmaleek sai April, watan haihuwa na kenan, yanzu kuma january muke.
Waliman kuwa yayi kyau amaryah ma tasha kyau sosai 
Bayan mun dawo ne da daddare mukaje duk muka gaida Bappanun mu nida hafsy da su Aunty B da suka sauƙa a ɗaya side ɗin da Abba ya gina, kusan ɗakuna 6 ne a wannan gidan, ɗakin ummie suka buɗe a ciki suka sauƙa,mamah ma a nata ɗakin ta sauƙa tare da hafsy, hajiya ummah kuma nata ɗakin tare da Aunty Rakiya da Aunty ma'u.
********* Washe gari tun ƙarfe 9:00am bata cika ba su Abba da dukka yayuna da ummie,mamie, raliya suka iso, mota Biyu sukayi suma, yayah Muhammad ke jan su Abba da su mamie da ummie, Abba ke zaune gaba tare da yayah da yake ja, baya kuma umie ne da mamie sai raliya,  ɗayan motan kuma Yayah Ahmad ne tare Da A.G a gaba, baya kuma M.G ne da heedayah sai babyn su  Affan.
Babban parlon side ɗin Abbah suka sauƙa, kuma nan aka kai abin breakfast, duka ƴan'uwan Abba sunzi sun gaisa, maza da mata da ƴaƴayensu, nidai parlon ummie muka zauna tare da A.G, daga bayane da suka shigo muka fice domin a basu wuri suyi break, parlon mamah duk muka koma, kuma har lokacin bamu haɗu da mamie ba.
Ƙarfr 11:00am aka ɗaura auren hadiza da suraj, kuma aranan zaayi wuni, kuma akaita family house ɗinsu suraj inda yayi ginin shi, washe gari da sassafe za'a wuce da ita kaduna inda gidan ta yake.
Anyi wuni mai daɗi cike da jin daɗin ganin ƴan'uwa  Abba da ƴan'uwanshi kaman bazasu rabu ba suke ji, ƙarfe biyar da kusan rabu Abba yace duk su ummie da suka zo tare yau su fito a wuce gida, har waje muka rako su, inda Abba yace ita Raliya ta zauna ta biyo mu gobe,  amma fir mamie taƙi, inda take cewa gobe wai da wuri zasu fita da surkuwarta, jin haka ne yasa Abba rabuwa da su, muna tsaye a waje ga mutane dayawa ana jiran fitowan Abba, kawai saiga mamie da raliya biye a bayan Abba suma sun fito, nidai ina tsaƴe gefen headayah rungume da Affan, gefe na kuma xainab ce a tsaye.
Wani irin Salati da mamie ta zabga ne ya bani tsoro, wanda ya jawo hankalin kowa kan ta,  "me nake gani tare da ayshaa kaman ciki? Yayah akayi kuma naga ciki"? Kalmar da ta fito da ƙarfi kenan a bakinta, hakan kuma ya jawo hankalin kowa zuwa gareni, nidai duk sai naji tsoro da kunya ya kamani,  "ikon Allah kuwa, wanda yake bayarwa a duk lokacin da yaji ya mishi, wanda yake hanawa a duk lokacin da yaji ya mishi, shi ya bata ya kuma tsare mata shi har ya kai haka, ba dabaranta babu ikonta, sai ƙarfin mulki irin na rabbil- izzati" Aunty Rakiya  ta faɗa tana karɓan Affan da yake hannuna, ko lura da irin tsoritan da nayi tayi, hala shiyasa ta karɓe yaron  ko kuma mamie ta samu daman ganin abunda ke cikin ne ohoo.
"Tou ae ban taɓa zato ko tunanin ayshaa zata haihu ba, na ɗauka ita da raliya sun gado mamah ne, abun ne yaban mamaki don ba haka aka gaya mun ba"  mamie ta sake faɗa cike da suɓutar baki,  dariya mai sautimamah tayi sannan tace,  "abu na Allah kuwa, ae shi baya shawara yake abun shi, gado kuma ae raluya ce kaɗai a gidan nan ta gado ni, nima Allah yasan dalilin daya sa bai bani ba, bawai shirkah ko tsafin mutane bane ya hanani, duk cikin rahamar shi yasa bai bani ba, kuma bana baƙin ciki, tunda yabawa mijina kuma Alhmdllh inaji kaman ni na haifah, bani da damuwa ko baƙin cikin komai, Ayshaa kuma Allah ya bata sai fatan Allah ya inganta shi ya sauƙe ta lafiya, Allah kuma ya kare mata daga sharrin ma sharranta". 
Tsawa Abba ya daka musu ganin zasu fara baza hali a wurin, ga surakunen shi ga ƴan'uwa da ƴan unguwa, ga kuma ya hango hajiya ummah ta fito, mota ya nuna wa mamie akan ta shige su tafi, aiko hajiya ummah ta iso wurin hafsy a bayanta, daga gani ita ta ƙirata, mitsi - mitsi tayi da ido tana kallin Abba tana maida kallonta kan mamie kuma,  "amma dai hauwa anyi mutuniyar banza anan, har yanzu usmanu bai ɗauki shawarana ya kai ki ƙasar india anmiki sabon ɗashen zuciyar ba ko? Tou aniyar ki ta biki, insha Allah khairan a gidan ayshaa babu sharran, sharran ya ƙare akanki da munafukar ƴarki da tayi saura, rashin haihuwa ba Allah yaƙi mutum bane sakarya abokiyar tafiyan shaiɗan, gaskiya kin cuci usmanu da yahaɗa zuriya da ke, tou ta Allah ba taki ba wuce da mummunar fuskar ki aniyarki ta biki ku tafi,"  sannan ta maida kallonta kan A.G tace,  "kai kuma ja matar ka ku tafi, ka kaita chan wurin dattijuwar kakarka kace inji ni a rubuce mata Tabara da yaseen, a ƙara da lahaula saboda sharrin bakun maƙiya, ni nan ina wurin bikin jikata ce, bazan samu zama da ita na saka a rubuce shi tsaff ba, inda hali qur'ani ma izzu sittin a rubucr mata, din sharrin matar usmanu yawa ne da shi".
Abba ne ya ƙurawa Aunty Rakiya ido ita kuma ta gane mai yake nufi, kamo hannun hajiya ummah da ta fashe da kuka tana tsinewa sharrin mamie tayi, haƙuri take bata akan su juya suje ciki, sannan tacewa A.G yayi haƙuri insha Allahu babu komai, zasu kula dani gobe da wurin za'a dawo.
Ajiyan zuciya yayi yana bina da kallo, hannu na za<nab ta riƙo muka koma gida ,  jama'a dai sai mamakin halin mamie kawai akeyi, haka suka tafi mu kuma muka dawo  gida.
Aiko suna isa bauchi a tsorace heedayah ta labartawa mummy, jiki na rawa mummy ta sanar da Daddah da Daddy, shi kanshi Daddyn ya umurci A.G ya koma ya ɗaukoni, babu inda xan kwana sai nan, haka ko akayi muna idar da sallan ishaa sai ga call ɗinshi, waje na futa cike da mamaki, ai kuwa ganin shi nayi a mota zaune shida M.G,
Buɗe mun sit ɗin baya yayi na shiga, sannan ya ɗaga waya ya ƙira hafsy,nidai bai wani sake fuska ba shiyasa ban iya mishi magana ba, sakata yayi ta tattaru mishi duka kayana yace ta kawo mota muna jiranta.
Dariya kawai Aunty Rakiya tayi lokacin da hafsy ta gaya mata xamu tafi, ita kuma Hajiya ummah da mamah daɗi abun ya musu, sai addu'a isa lafiya kawai suke mana.
Banso ba don banyi sallama da kowa ba, hattah hadiza bamu haɗu ba, akan zamu zo gidan ta idan mun gama, don banje kai amaryah ba akan daga baya sai muje.
Haka yaja motan shiru baya kula owa, A.G dai nada dana sani ya koma mun, sai M.G ne kawai yake ɗan hira dani jifa-jifah, shima ganin nakasa nutsuwa ya saka ya rabu dani.
Fadaman mada Mukaje Gidan su A.G, har waje mummy da heedayah suka fito taryan mu, ina ankare da mummy yadda hankalinta yake tashe, fitowa tayi ta riƙo hannun na muka shige parlor, ita kuma heedayah ta karɓi kayana da yake hannun A.G.
*AUNTY NICE*