Ko Kasan Amfanin JAN BAKI A Cikin  kwalliyar Mata?

Saboda Muhimmanci Jan Baki, a wani shuɗaɗɗen zamani kafin zuwansa a cikin samfura kala-kala na Zamani, Mata sukan ci fure don bakinsu ya yi ja, haka kuma suna amfani da fure su goga a leɓensu don armasa kwalliyarsu. Shafa jan baki yana ƙarawa kwalliya armashi ainun, saboda zan iya cewa ido da baki ne ke fito da kyawun kwalliyar da mace ta yi.

Ko Kasan Amfanin JAN BAKI A Cikin  kwalliyar Mata?

Ko Kasan Amfanin JAN BAKI A Cikin  kwalliyar Mata?

 

Daga Rukayya Ibrahim Lawal

JAN BAKI: Wani sinadari ne da ke ƙarawa kwalliyar mata kyau da armashi, kuma akwai sirrin jan hankali a tattare da shi a tsakanin al'umma maza da mata.
 
Duk kwalliyar da ba Jan Baki a cikinta ba ta kai kwalliya ba, mata da kansu ba su ji a jikinsu sun yi kwalliyar burgewa da cakirewa ta fita tsara matukar lebban mace ba su da wannan sinadarin jan.
 
Saboda Muhimmanci Jan Baki, a wani shuɗaɗɗen zamani kafin zuwansa a cikin samfura kala-kala na Zamani, Mata sukan ci fure don bakinsu ya yi ja, haka kuma suna amfani da fure su goga a leɓensu don armasa kwalliyarsu.
 
Shafa jan baki yana ƙarawa kwalliya armashi ainun, saboda zan iya cewa ido da baki ne ke fito da kyawun kwalliyar da mace ta yi.
 
Shafa jan baki ya kan sa mace ta yi kyau, kuma kwalliyarta ta ƙara kyau da ita sosai.
 
Jan baki yana ƙara fito da sirrin kyawun kwalliyar mace, yana saisaita baki sosai, sannan ana bin matching colours saboda Mace ta ƙara fitowa cas abinta.
 
Zancen Gaskiya fa Jan baki nada tarin muhimmanci da amfani ga kwalliyar mata, bayan fito da kwalliyar mace yakan hana mata bushewar lebo.
Jan Baki na sanya wa mata karsashi da zama a cikin nutsuwa don tana ji da kanta a matsayin wata da ta burge hakan sai ta dire kar reni ya zo a kusa da ita.