Gwamnatin Kano za ta dauki sabbin malaman makaranta 4,000
Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Kano (SUBEB), Yusuf Kabir, ya ce hukumar na shirin daukar karin malamai 4,000 domin karfafa koyar da karatu Matakin farko da lissafi a kananan hukumomi 44 na jihar.
Ya bayyana hakan ne a taron bitar sakamakon kimanta karatun dalibai na ƙarshen shekarar 2025, wanda aka shirya domin tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ci gaban koyon dalibai a karkashin shirin Partnership for Learning for All in Nigeria (PLANE) na tsawon shekaru uku, wanda gwamnatin Birtaniya ke tallafawa.
Kabir, wanda sakatariyar hukumar, Hajiya Amina Umar, ta wakilta, ya bayyana cewa duk da cewa malamai 4,343 aka dauka a karin daukar ma’aikatan baya-bayan nan, har yanzu jihar na fama da karancin malamai.
“Mun mika bukata ta hukuma domin daukar karin malamai 4,000, kuma masu neman aikin suna da yawa. Tuni mun fara shirya cibiyoyin CBT guda bakwai a Wudil, Bichi da wasu wurare domin gudanar da jarabawar cancanta,” in ji shi.
A cikin sabbin gyare-gyaren da ake shirin aiwatarwa, jihar na kokarin rage cunkoson aji daga tsarin malami daya kan dalibai 132 a wasu ajujuwa zuwa burin samun malami daya kan dalibai 60.
Wani mai ruwa da tsaki, Dr. Miswaru Bello, ya bayyana damuwa cewa kashi 40% na daliban Kano ba sa halartar aji, yayin da rashin halartar malamai ke kaiwa kusan kashi 12%.
managarciya