Cire Sarakuna Gwamnatin Sakkwato Ta Yi Daidai?

Cire Sarakuna Gwamnatin Sakkwato Ta Yi Daidai?

Gwamnatin Sakkwato karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto ta bayar da sanarwar dakatar da Sarakuna uwayen kasa a jiha su 15 a jiya Talata abin da ya zama abin magana a tsakanin mutanen gari.

Sarakunnan da tsohuwar Gwamnatin Sanata Aminu Waziri Tambuwal ta nada ne abin ya shafa in ka cire Sarkin Kabin Yabo da suke da tsohuwar tankiya a tsakaninsa da wani jigo a siyasar jiha.

An samu Bambancin ra’ayi a tsakanin mutanen jiha in da wasu ke ganin matakin da gwamnatin Sokoto ta dauka ya yi daidai  yayin da wasu ke ganin sam hakan bai dace ba, karanta ce kawai aka nuna.

Masu ganin yayi daidai suna danganta lamarin ne da bai kamata sarakuna su rinka sanya kansu a cikin harkokin siyasa  da nuna goyon bayan wani bangare tare da jingine wani gefe ba, wanda hakan zai sa duk wanda ya yi nasara sabanin wanda suka marawa baya ba za su tafi da su ba.

Masu ra’ayin na ganin ba a yin gwamnati da makiyi dole a nuna masa hanyar fita waje don ba za a bari a sha lagwadar gwamnatin da ba a kafa da shi ba.

A gefen wadan da ke ganin gwamnatin Sokoto ta tabka mugun kuskuren da zai bi ta har karshen wa’adin mulki, ba a kirkira makiyi da gangan a harkar siyasa, kuma duk dan siyasar da ke da halin rashin yafiya duk yanda yake ganin ya samu nasara tana da nakas a duk sanda aka yi nazarin kwakwaf.

A duk sanda dan siyasa ya yi nasara ya koma duban yanda zai karya abokan hamayyarsa ta hanyar musguna masu ka tabbatar ya jawowa kansa aikin wahalar da ba zai kare ba.

Cire sarakuna ba daidai ba ne domin su masu biyayya ne ga duk gwamnatin da ke ci a jiha, babu hujja a lokacin da kake adawa ka ce sarki sai ya goya maka baya ya bar gwamnatin da ke kan mulki in bai yi hakan ba, ka mayar da shi abokin gaba da zai sa har ka raba shi da rawaninsa.

Abin da zai kara fito da rashin cancantar abin da gwamnati ta yi ya nuna wadan da ba a taba ba kenan sun goyi bayan tafiyar gwamnati a lokacin da take adawa, gwamnatin da ta kyale su kenan ba ta san ba su goyon bayan ta ba ne ko kuma sun kyale su ne domin hali na kawaici da dattako.

Matukar Gwamnatin Sokoto ta dauki halin cin zarafi da musgunawa za ta Tarawa kanta makiya da za su yi kokarin yakarta a gaba, irin wadan nan makiyan suna da wahalar murkushewa domin suna yi ne don huce haushi  ko da sun san ba za su yi nasara, ba za su taba bari ba.