Karancin Sadaki Ya Yi Tashin Gwauron Zabo  Yanzu Ya Koma N48,985 a Najeriya

Karancin Sadaki Ya Yi Tashin Gwauron Zabo  Yanzu Ya Koma N48,985 a Najeriya
 

 

A ranar Juma'a, 12 ga watan Dhul Hijjah Hijira 1444, wacce ta yi daidai da 30 ga watan Yunin 2023, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar nisabin Zakkah, Sadaki da Diyyar rai. 

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu kacal da gudanar da idin babbar Sallah da aka gudanar a ranar Laraba 10 ga watan Dhul Hijjah na wannan shekarar. 
A sanarwar da sarkin Musulmin ya fitar, wacce hukumar kula da ganin jinjirin wata ta yada a shafinta na Facebook, an bayyana adadin kudade ga kowane bangare. 
A cewar sanarwar, yanzu nisabin Zakkah ya koma N3,918,800, wanda aka kwatanta da darajar farashin Gwal a duniya.
A bangaren haddin sata da kuma sadaki na auren mace, dole sai ya kai akalla N48,985 kafin ya cika ka'idar shari'a. 
Abin da hakan ke nufi shi
ne, ana yanke hannun barawo ne idan a shari'ance idan ya saci dukiyar da ta kai aalla N48,985. 
Hakazalika, a shari'a dole mai neman aure ya ba da sadakin da bai yi kasa da N48,985 ba don cikar ka'idar daurin aure. 
A bangaren Diyyar rai, ana daurawa wanda ya yi kisa biyan Diyya ne a kan kudi N195,940,000, duba da darajar kudade da ake dasu a yanzu.