Yakamata Zaben Nijeriya Ya Zama Bai Daya---Jonathan 

Yakamata Zaben Nijeriya Ya Zama Bai Daya---Jonathan 

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya nemi majalisar tarayyar ƙasar ta mayar da lokutan zaɓen gwamna lokaci ɗaya a ƙasar ba tare da ware wasu ba kamar yadda ake yi a yanzu.

Jonathan ya yi kiran ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da ke gudana a yau Asabar tare da na jihohin Kogi da Imo.

"Idan muka ci gaba da yin irin wannan zaɓen na bayan babban zaɓe saboda shari'o'i to wata rana shi ma zaɓen shugaban ƙasar Najeriya zai sauka daga lokacin da aka saba yin sa," in ji shi.

Ya bayar da misali da zaɓen shugaban ƙasa na 2007, inda ya ce alƙalan kotun ƙoli uku cikin bakwai ne suka ce a sake zaɓe, yayin da huɗu suka amince da sahihancinsa.

"Da a ce alƙali ɗaya ya bi sawun waɗanda suka ce a sake zaɓe da tuni zaɓen shugaban ƙasa ya sauka daga kan lokacin da aka saba yin sa."

Jihohin sun sauka daga layin lokacin da aka saba gudanar da babban zaɓe ne saboda hukunce-hukuncen kotu da ke ƙwacewa ko kuma su bayar da umarnin a sake zaɓe a jihohin.

Akwai jihohi bakwai da ba su yin zaɓen gwamna tare da saura a Najeriya, waɗanda suka haɗa da Kogi, da Imo, da Bayelsa, da Edo, da Anambra, da Osun, da Ekiti.