IBB Zai Shiga Tsakani Don Sulhunta Atiku da Gwamnoni 5 Masu Yiwa PDP Barazana 

IBB Zai Shiga Tsakani Don Sulhunta Atiku da Gwamnoni 5 Masu Yiwa PDP Barazana 

Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa, tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya zai shiga tsakanin don warware rikicin cikin gida da PDP ke ciki. 

Jaridar Leadership ta tattaro cewa, tsohon shugaban na Najeriya zai yi wata ganawa da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da gwamoni biyar da ke adawa da ta tsarin shugabancin PDP da ake kira G-5 a birnin Minna ta Neja ranar Juma'a. 
Wannan ganawa ta IBB da su Atiku za ta zo ne kwanaki uku bayan da ya zauna da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu. 
Majiya ta nuna cewa, shiga tsakani da IBB zai yi ya zo ne daga shawarin wasu manyan tsofaffin shugabannin soja daga yankin Arewacin Najeriya masu goyon bayan Atiku, Naija News ta tattaro. 
  Har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana tsakanin gwamonin G-5 da Atiku a yunkurinsu na ganin a tsige shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Iyochia Ayu tare da maye gurbinsa da dan Kudu. 
Wannan rikici ya faro ne ta bangaren gwamna Wike, wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin da PDP ta gudanar a watannin baya da suka gabata.