Ta Bankawa Kanta Wuta Bayan Mijinta Ya Sake ta

Ta Bankawa Kanta Wuta Bayan Mijinta Ya Sake ta

Daga: Abbas Yakubu Yaura.

Wata mata ‘yar shekara 40 (an sakaya sunanta) ta cinna wa kanta wuta bayan mijinta ya sake ta a karamar hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Dutse ranar Juma’a.

Shiisu ya ce matar da ke zaune a kauyen Garin Mallam ta zuba man fetur a jikinta sannan ta bankawa kanta wuta.

“A ranar Alhamis, da misalin karfe 07:40, rundunar ta samu labari mai ratsa zuciya da ban tausayi na wani lamari da ya faru daga Garin Guri, wanda ya nuna cewa wata mata ‘yar shekara 40 a kauyen Garin Mallam ta zuba man fetur a jikinta, ta kona kanta, kuma ta kone fiye da kima wanda hakan ya yasa ba za a iya gane ta ba.

An rawaito cewa ta hallaka kan nata ne a wajen kauyen.

“Bayan samun wannan rahoto, tawagar jami’an hedikwatar ‘yan sanda ta Guri sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka tabbatar da faruwar lamarin.

“Jami’an sun kai gawar zuwa asibiti, daga baya kuma suka mika gawar ga ‘yan uwanta domin yi mata jana’iza,” in ji Shiisu.

Ya bayyana cewa binciken farko da aka yi ya nuna cewa marigayiyar ta samu bakin ciki bayan wasu watanni bayan rabuwar ta da mijinta.

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Ahmadu Abdullahi, ya shawarci mutane da su mika al’amuransu ga Allah Ta’ala domin samun mafita a duk Lokacin da suka tsinci kan su a wani Mawuyacin hali.

Abdullahi ya kuma shawarci jama’a da su rika neman shawarwari da nasiha daga dattawan su kan al’amura masu sarkakiya don gujewa faruwar irin wannan lamari. (NAN)