Tsohon Gwamnan Sakkwato Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya ba da biliyan ɗaya ga mutanen jihar Sakkwato domin rage masu raɗaɗin talauci da suke ciki.
Tsohon Gwamna Bafarawa ya yi bayanin ne a wurin ƙaddamar da Gidauniyarsa da za ta raba kuɗin ga mabuƙata a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar Zakka da waƙafi na jiha Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, a gidansa ranar Laraba data gabata, ya yi godiya kan damar da mutanen Sakkwato suka ba shi kan haka zai ci-gaba da hidimta masu har abada.
"A shekarun da na shafe a matsayin gwamna na yi ƙoƙari wajen ganin an samu gajiyar dimukuradiyya ga al'umma, gwamnatina ta samu nasara wajen aiyukkan raya kasa musamman shimfiɗa hanyoyi da inganta kiyon lafiya da raya ilmi, hakan ya sa na tabbatar da an yi amfani da dukiyar Sakkwatawa yanda Yakamata.
"Idan na tuna soyayyar da Sakkwatawa suka nuna min sai na so na wuce abin da na yi a yanzu, la'akari da yanda aka tafiyar da gwamnati ana iya samun kuskure hakan ke sa akwai bukatar kawo irin wannan sauyi don samun rabo a wurin Allah, abin da ya bani azama na rama alheri da Sakkwatawa suka yi min ba tare da la'akari da duk wani alheri dana yi a lokacin da nake gwamna.
"Alaka ta da Sakkwatawa ba zan taɓa mantawa da ita ba shekaru 17 bayan na sauka Gwamna ina murna da farin cikin ganin al'umma ba ta sauya ba, zamana dan shekara 70 da haihuwa burina na cika duk wani giɓi da aka samu a dangantaka ta da al'umma. Wasu za su kira wannan a matsayin neman afuwa amma na fi son a dubi rama alheri ne da alheri na soyayyar da aka nuna min kuma yanzu ne yafi da cewa a lokacin da jama'a ke cikin halin matsi hakan ya sa na fitar da kudi naira biliyan ɗaya don ganin an samar da jin dadi da walwalar Sakkwatawa," kalaman Bafarawa kenan.
Ya juya kan kwamitin da ya samar ya ce shugaban kwamitin ya amince da rikon amanar sa kuma sananne ne a wurin gudanar da irin wadan nan aiyukkan, shirin tallafin zai zagaye dukkan ƙananan hukumomin Sakkwato, za a mayar da hankali wurin samar da abinci ruwan sha da sutura ga mutanen jiha.