'Yan bindiga sun saki ɗaliban da suka sace a Zamfara su 75
Gwamnatin Jihar Zamfara da haɗin guiwar Jami'an Tsaro sun yi Nasarar kuɓutar da ɗaliban Makarantar Je ka Ka dawo ta garin ƙaya tare da Malamansu wadanda 'yan bindiga su ka yi garkuwa da su a makonnin da su ka gabata.
Dalibbai 75 da Wasu Malaman su da 'yan bindiga suka ɗauka a Zamfara Sun Kubuta ne a yau Lahadi"
Rahotanni daga jihar Zamfara na nuna cewar, dalibban makarantar sakandari ta jeka ka dawo GDSS na garin Kaya dake karamar hukumar Maradun sun kubuta tareda malaman su bayan da 'yan bindiga suka dauke su a kwanakin baya.
An tattaro cewar, kawo yanzu dukkan dalibban sun kubuto kuma tuni suna a gidan gwamnatin jihar ta Zamfara domin yin wasu jawabai.
Bayanai sun tabbatar da cewar, an kubutar da dalibban ne biyo bayan matsin da 'yan bindigar kan samu a dazukan jihar tare kuma da kokarin gwamnatin jihar.