Gwamnatin Borno Ta Mayar  Da Yan Gudun Hijira Mutum 632 Zuwa Gidajen Su Tare Da Raba Masu Kudade Da Kayayyaki Na Miliyoyin Nairori

Gwamnatin Borno Ta Mayar  Da Yan Gudun Hijira Mutum 632 Zuwa Gidajen Su Tare Da Raba Masu Kudade Da Kayayyaki Na Miliyoyin Nairori

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

A yau Laraba ne gwamna Farfesa Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya maida wasu 'yan gudun hijira mata da maza mutum (632) zuwa gidajen su a kauyen Malari dake karamar hukumar Konduga ta jihar Borno. 

Daga cikin 'yan gudun hijirar da gwamnan ya maida su gidajen su sun hadar da maza 250 da kuma mata 379.

A yayin bikin maida mutanen gidajen su, Gov. Babagana Zulum, ya ce al'ummar sun koma gidajen su ne bayan shafe tsawon shekaru 7 da 'yan ta'addan Boko Haram suka kore su daga gidajen su.

Ya ce yau an maida su gidajen su ne bayan da gwamnatin jihar Borno ta gina masu gidaje 803 wanda 'yan ta'addan Boko Haram din suka lalata masu.

Gwamnan ya kuma sanar da bada tallafin kudi maira dubu 20 ga dukkan mazaje da kuma naira dubu 10 ga matan da aka maida gidajen su a yau Laraba.

Farfesa Babagana Umara Zulum,  ya kuma bada umurnin a bada kyautar kudi naira dubu  dari-dari (100) ga mutum 500 a kauyen Malari wadanda gidajen su basa cikin gidaje 803 wadanda gwamnatin Borno ta gina masu.

Zulum, ya kuma raba masu kayan abinci da suturu wanda hukumar cigaban yankin Arewa maso gabas (NEDC) ta bayar domin a tallafawa al'ummar garin.