Yanda Ake Gyaran Fuska Da Tumatir Ta Yi Sheki Da Kyau

Da yawa daga cikin ku za su yi mamakin Tumatur dai tumatur ɗin nan da ake miya da shi ko kuwa wani tumatur ɗin daban?.

Yanda Ake Gyaran Fuska Da Tumatir Ta Yi Sheki Da Kyau


Da yawa daga cikin ku za su yi mamakin Tumatur dai Tumatur ɗin nan da ake miya da shi ko kuwa wani Tumatur ɗin daban?.

To amsar ɗaya ce Eh Tumatur ɗin da ake miya da shi 'yar uwa.


Da farko za ki sami Tumatur ɗinki, mai kyau nunanne. Idan nace mai kyau ina nufin jajazur ɗin nan fa, wanda ya cika ya batse, bame ruwa ba.

Za ki fasa shi ki cire 'ya'yan dake cikinsa.

Bayan kin tabbatar kin cire dukkanin 'ya'yan sai ki shafawa fuskar ki wannan Tumatur ɗin. Tsawon mintuna sai ki wanke.

'Yar za ki sha mamaki, domin kuwa lokaci ɗaya fuskarki za ta canja ta yi gwanin kyau, haka zalika idan kina da ƙurajen fuska suma za su mutu.

Wannan hadin kusan mu jarabun ne a cikin mata da yawa an gwada shi kuma an yi nasara musamman mata masu bukatar fuskarsu ta sumul duk wani ciwo ya cire a saman fuskarsu.
DOCTOR MARYAMAH.