Rufe Boda Da Buhari Ya Yi Tun Da Farko Shine Silar Fadawar Ƴan Nijeriya Cikin Matsin Rayuwa

Rufe Boda Da Buhari Ya Yi Tun Da Farko Shine Silar Fadawar Ƴan Nijeriya Cikin Matsin Rayuwa

Daga Bashir Abdullahi El-bash.

Ni dai na kasa fahimtar hikimar da ke tattare da rufe boda. Domin daga lokacin da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya rufe boda ƴan Najeriya suka faɗa cikin ƙunci, matsi da tsadar rayuwa gami da hauhawar farashin kayayyakin masarufi. Duk abin da kake saya kafin rufe boda wani ya ninka fiye da sau goma bayan rufe boda.

Buhari ya bayyana cewa ya rufe boda ne domin ƴan Najeriya su noma abin da za su ciyar da kansu, amma ni a fahimtata naso ace kafin ya bar mulki ya buɗe bodar tunda a madadin a samu sauƙi tsanani ne ya ƙaru bayan rufe bodar.

Haka zalika ya ce ya rufe boda ne saboda ƴan Najeriya su koma gona, amma a madadin abincin da sauran kayayyaki su yi sauƙi sai matsala ta ƙaru saboda manoman Najeriya ba za su karya kayansu su sayar a farashi mai sauƙi ba saboda sun riga sun san ba wani kaya da yake shigowa cikin ƙasar daga ƙasashen waje.

Ni a fahimtata tun farko wannan ita ce matsalar, a madadin Buhari ya buɗe boda kafin ya bar mulki tunda ba ta yi wani tasiri ba sai ya tafi ya bar boda ta cigaba da zama a rufe kayayyakin masarufi suke cigaba da tashi ƴan Najeriya suke cigaba da kokawa.

Nauyi ne a wuyan shugaba idan ya ɗauki wani mataki ya ga babu cigaba to ya sauya tsari. Tunda an rufe boda an ga ba ta yi wani tasiri kan samar wa ƴan Najeriya sauƙi ba to kamata yayi tun kafin ya bar mulki ya buɗe ta.