Farfesa Aisha Bawa: Abin Farinciki Ya Saamu Al'ummar Yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara

Farfesa Aisha Bawa ita ce mace ta farko a sashen ilimin nazarin Tarihi a Jami'ar Usmnan Danfodiyo da ta samu wannan girman na zama Farfesa abin da ya kara sanya farinciki a cikin zukatan al'umma,

Farfesa Aisha Bawa: Abin Farinciki Ya Saamu Al'ummar Yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara

Farin ciki ya mamaye al'ummar yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara a lokacin da labarin amincewar  zama Farfesa ga Hajiya Aisha Bawaya sami mutane.

Majalisar jami'ar Usman Danfodiyo ta yi karin girma zuwa matakin Farfesa ga Aisha Bawa(Professor of Gender History).
Wannan lamari ne na musamman ganin yadda jajarcewarta da sadaukarwarta da aiki tukuru da take yi ba su tafi a banza ba, kudirinta a fannin koyo da koyarwa sun tabbata.
Shahararta ya kara bunkasa a lokacin da take rubuce-rubuce don fito da kimar mata da kokarinta na su san kansu a wannan lokaci da ake yi masu barazana daban-daban. 
Farfesa Aisha Bawa ta halarci tarukka daban-daban a Nijeriya da kasashen waje a fadin Duniya, ta shirya taron kasa da kasa kan mata da yanayinsu a cikin tarihi wanda aka yi a shekarar 2019, ta rubuta littafi kan rawar uwar gidan Shugaban kasar Nijeriya da aka yi a tarihi.  
Bayan gudunmuwarta a fannin karatu da karantawa tana tausayin dalibbanta kwarai da gaske hakan ya sanya  har suka rada mata sunan 'YAR ALJANNAH, ta ba da gudunmuwa sosai a kungiyoyin malaman jami'a kwarai da gaske, halinta ya sauya tunanin yanda ake kallon mata a Arewacin Nijeriya musamman a fanin ilimin zamani.
Farfesa Aisha Bawa ita ce mace ta farko a sashen ilimin nazarin Tarihi a Jami'ar Usmnan Danfodiyo da ta samu wannan girman na zama Farfesa abin da ya kara sanya farinciki a cikin zukatan al'umma, an yi ta yi mata fatan alheri da karin samun cigaba a rayuwarta gaba daya.
'Yar asalin jihar Kebbi ce da yankin ta ke tinƙaho da ita.