Rasuwar Ahmad Tage ta girgiza masana'antar Wasan Hausa

Ya fi fitowa a finafinan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro a harkar wasan.

Rasuwar Ahmad Tage ta girgiza masana'antar Wasan Hausa
Rasuwar Ahmad Tage ta girgiza masana'antar Wasan Hausa

Rasuwar Ahmad Tage ta girgiza masana'antar Wasan Hausa

'Yan wasan Hausa dake masana'antar Kannywood sun yi alhini tare da kaduwar daya daga cikinsu.

Ahmad Tage ya rasu ne bayan jinyar rashin lafiya a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano.

Ya fi fitowa a finafinan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro a harkar wasan.

'Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 21.

Fitaccen jarumi Ali Nuhu ya sanar da labarin mutuwar Ahmad Tage a shafinsa na Instagram tare da yi masa rokon gafarar Allah

Taurari da sauran masu ruwa da tsaki a Kannywood da dama ne suka bayyana alhinin rasuwar Ahmad Tage.

Taurari irin su Saratu Gidado Daso da Maryam Booth da Abdullahi Nuhu da mawaƙa irin su Ado Gwanja sun yi wa mamacin addu'ar Allah ya jikansa.

A sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, Jaruma Saratu Daso ta ce mamacin wanda darakta ne kuma Jarumin kuma mai ɗaukar hoto ya rasu ne a ranar Litinin din nan.