Shugaban EFCC ya caccaki ƴan Nijeriya kan kare shugabanni masu cin hanci

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya ce ‘yan Najeriya na sukar cin hanci da rashawa amma suna goyon bayan shugabanni masu laifi yayin da ake gurfanar da su a kotu.
Olukoyede ya bayyana hakan ne a jiya Juma’a a Abuja yayin da jami’an Cibiyar Sadarwa da warware rikici ta (CCC), karkashin jagorancin Chris Olukolade, daraktan kwamitin amintattu na cibiyar, su ka kai masa ziyara.
Shugaban na EFCC ya ce idan kowa ya dauki rashawa a matsayin abokiyar gaba gaba, rashin ci gaba zai zama tarihi a kasar.
“Daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban Najeriya ita ce cin hanci da rashawa, kuma idan aka magance ta, rashin ci gaba zai zama tarihi,” in ji Olukoyede.
“Duk al’ummar da ke son ci gaba ba alhakin gwamnati kadai ba ne zai sa ta samu wannan ci gaba, har da na ‘yan kasa gaba daya," in ji shi