Har Abada, Malamin Allah Ba Zai Taba Hada Kai Da Azzalumai A Cuci Kasarsa Da Talakawa Ba!
A koda yaushe, Malaman Allah, malaman gaskiya, ana tsammanin cewa su zamo masu gaskiya, masu adalci, masu tawali'u a cikin harkokin iliminsu da rayuwarsu, kuma su zamo masu kare gaskiya, kuma masu taimakon gaskiya da masu gaskiya a duk inda suke.

Daga Imam Murtadha Gusau
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum
Kwanan nan, wata takaddama mai zafi sosai ta kunno kai, akan cewa wai shugabanni suna hada kai da Malaman addini ana ruguza kasa, ko shugabanni suna hada kai da Malamai ana cutar al'ummah.
Eh, mu ba ma yin musun cewa lallai Malaman addini sun kasu gida biyu; akwai Malaman Allah da Annabi, haka kuma akwai miyagun Malamai a cikin al'ummah, wadanda suke yin amfani da addinin Allah suna cuta da zalunci iri-iri, kala-kala. To amma duk da haka, mu munyi imani da Allah cewa, shi Malamin Allah da Annabi, babu yadda za'a yi ya amince, har ya shiga cikin duk wata irin hanya, wadda za ta zama sabanin hanyar Allah da Manzanninsa.
Sannan hakika a Musulunci, Malamai suna da matukar daraja da muhimmanci da girma sosai a wurin Allah da kuma al'ummah, kuma hakika Malamai suna taka muhimmiyar rawa wurin ba wa addinin Allah kariya da fassara shi da bayyana shi ga mutane, tare kuma da yada shi gwargwadon karfinsu da ikonsu. Kuma Musulunci ya tabbatar da cewa Malamai magada Annabawa ne, kuma Allah Subhanahu wa Ta'ala ya dora hakkin jagorancin al'ummah a kan su, musamman dangane da shiryar da al'ummah zuwa ga Musulunci, da abunda ya shafi imaninsu, da sanin hukunce-hukuncen addini, da dabi'u da halayensu, da ruhinsu da sauransu.
A koda yaushe, Malaman Allah, malaman gaskiya, ana tsammanin cewa su zamo masu gaskiya, masu adalci, masu tawali'u a cikin harkokin iliminsu da rayuwarsu, kuma su zamo masu kare gaskiya, kuma masu taimakon gaskiya da masu gaskiya a duk inda suke.
Ana tsammani daga Malaman Allah, su tashi tsaye haikan, su yaki zalunci da azzalumai, a bisa duk wata hanya da Shari'ah ta tsara.
Malaman Allah, mutane ne wadanda babu yadda za'a yi ka same su suna yarda da zaluncin masu zalunci, balle ace su hada kai da su a rusa kasa ko a cuci bayin Allah talakawa.
Musulunci ya dauki harkar ilimi da girma, bai yarda ayi saku-saku da hanyar ba, ko kuma a aikata abun da zai jawo sanadiyyar lalacewar hanyar. Kuma Musulunci yayi kira ga muminai da suyi kokari su gane Malaman Allah, domin suyi masu da'a da biyayya. Kuma su gano miyagun Malamai, domin su guje su, su kaurace masu, kuma suyi Allah waddai da su.
Na daga cikin hanyoyin gano Malaman Allah:
1. Malamin Allah dole ya zamo mai ilimi da kwarewa akan harkar ilimin. Ya san zancen Allah (Alkur’ani) da zancen Manzon Allah (SAW) wato Hadisi, da maganganun Malamai magabata, da irin yadda suka fassara, tare da yin bayani akan nassoshi.
2. Malamin Allah dole ya zamo mai gaskiya da rikon amanah. Ya nemi ilimi domin Allah da neman yardar Allah, da kuma nufin kawo gyara da ci gaba mai amfani a cikin al'ummah. Kar ya zamo ya nemi ilimi ne domin neman suna, ko neman shahara, ko neman wani abun duniya mai karewa.
3. Dole ne Malamin Allah ya zamo mai halaye nagari, mai dabi'u masu kyau, mai tawali'u, mai kokarin koyi da Manzon Allah (SAW) a cikin halayensa da dabi'unsa, da cikin dukkanin lamurransa.
4. Ana sa rai Malamin Allah ya zamo mai tsantseni da taka-tsan-tsan da kiyayewa wurin bin Alkur’ani da ingantacciyar Sunnar Manzon Allah (SAW). Ba zaka same shi yana kokarin kirkiro abun da yake tsakaninsa da Allah ya san cewa wannan abun ba addini bane.
5. Kar Malamin Allah ya yarda, ko ta wace hanya, a same shi cikin wata badakala ta rashin gaskiya, ko ha'intar al'ummah, ko a hada kai dashi a cuci al'ummah ko a zalunce su.
6. Ba laifi bane Malami yayi kwalliya, yayi ado, ya gina gida mai tsada, ya hau mota mai tsada, ya auri mace kyakkyawa, musamman idan Allah Subhanahu wa Ta'ala ya hore masa ta hanyar halal. Amma ba daidai bane Malami ya zamo mai kwaikwayo da gasa da 'yan duniya, wurin kokarin tara abubuwan da na ambata a sama. Ana so Malamin Allah ya zamo mai tsantseni da gudun duniya, a bisa hanyar da Shari'ah da tsara. Kuma ya zamo mai yin hakuri da Dan abun da Allah Subhanahu wa Ta'ala ya bashi. Kar ya zamo mai hadama, mai handama da babakere, mai son yaci shi kadai, mai neman abun duniya ido-rufe, mai yaki-halal yaki haram.
Allah Subhanahu wa Ta'ala yace:
"Ya wadanda suka yi imani! Lallai ne masu yawa daga cikin Malamai, Ahbar da Ruhbanawa, hakika suna cin dukiyar mutane da zalunci da karya, kuma suna kange mutane daga bin hanyar Allah. Kuma wadanda suke taskancewar zinariya da azurfa, kuma ba su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi masu bushara da azaba mai radadi." [Alkur’ani, 9:34]
Kuma Manzon Allah (SAW) yace:
"Akwai wani abu da nike ji wa al'ummah ta tsoro, fiye da yadda nike ji masu tsoron masifar Dajjal: "ina ji masu tsoron Miyagun Malamai a cikin al'ummah." [Ahmad ne ya ruwaito shi]
Abdullahi Dan Amr ya ba da labari, yace Manzon Allah (SAW) yace: "Mafi yawan munafukan al'ummah ta sune makarantan ta (wato miyagun Malamanta)." [Ahmad ne ya ruwaito shi]
Manzon Allah (SAW) yace:
"Miyagun Malamai sune suke bin gidajen azzaluman shugabanni. Amma shugabanni na kwarai kuwa, sune suke bibiyar gidajen Malamai." [Ibn Majah ne ya ruwaito shi]
Umar Dan Khaddab (RA) yace, Manzon Allah (SAW) yace:
"Hakika, daga cikin abubuwan da nafi ji wa al'ummah ta tsoro, shine munafuki da ilimi a harshensa." [Ahmad ne ya ruwaito]
Annabi Muhammad (SAW) yace:
"Ko shakka babu, Allah yana son shugabannin da suke kusantar Malaman Allah, kuma suke yin hulda da su. Kuma Allah yana kyamatar Malaman da suke bibiyar gidajen masu mulki. Domin idan Malamai su suke bibiyar masu mulki, to Malaman zasu lalace, su karkata zuwa ga son abun duniya. Amma idan masu mulki su ne suke bibiyar Malamai, to masu mulkin zasu karkata zuwa ga lahira, tsoron Allah ya kama su, suyi wa talakawansu adalci." [Imamu Dailami ne ya ruwaito shi]
Ubadah Bin Samit (RA) yace:
"Idan Malami ya kasance mai bibiyar gidajen masu mulki, to zai zama munafuki, idan kuma yana bibiyar gidajen masu kudi, to zai aikata riya." [Duba Ihya Ulumud din, na Imamu Ghazali]
Ka'ab Ibn Ujrah (RA) ya ruwaito, Manzon Allah (SAW) yace:
"Hakika, wasu irin shugabanni zasu bayyana a bayana. Duk wanda ya bibiyi gidajensu da wurarensu, to dole ne ya amince da karyar da suke akai, kuma dole ya goyi bayan zaluncinsu. (Annabi yace) Basu tare da ni, ni ma bani tare da su; kuma ba za su sha ruwan tafki na ba. Sannan duk wanda bai bibiyi gidajensu ba, bai goyi bayan zaluncinsu ba, bai goyi bayan karyar su da yaudararsu ba, to ina tare da su, su ma suna tare da ni, kuma zasu sha ruwa a tafki na." [Tirmizi ne ya ruwaito shi]
Idan mun fahimci wadannan nassosa, zamu gane irin yadda addinin Musulunci yayi bayani filla-filla game da wannan mas'ala.
Don haka ya zama wajibi al'ummah ta san abun da take yi. Mu kusanci Malaman Allah, kuma mu kauracewa miyagun Malamai a duk inda suke. Sannan ya zama dole, kuma tilas, mu guji yin makauniyar biyayya ga ko wane Malami. Wallahi, a Musulunci babu girmamawa, babu da'a, babu biyayya ga duk Malamin da zai yarda ayi amfani da shi a cuci kasa, ko a cuci al'ummarsa.
Duk Malamin da yazo da gaskiya ya zama wajibi mu saurare shi, mu bi shi, muyi masa da'a da biyayya. Haka nan duk Malamin da yazo da shirme kuwa, wallahi ya zama tilas mu guje shi, kuma mu bar masa shirmensa.
A addinin Musulunci, baya yiwuwa kawai don mutum yana Malami, kawai ya zamo yana hada kai ana ruguza kasa, ana cutar da al'ummah, kuma mu rungume hannuwa, muna yi masa makauniyar biyayya, kawai don yana Malamin addini.
A tarihin Musulunci, anyi miyagun Malamai, to sai mu duba, yaya addini yace ayi dasu?
Gaskiyar magana ita ce, duk Malamin da ya bar hanyar Allah da Manzonsa, to wallahi wannan Malamin ya rasa wannan rigar tasa ta kariya, wato rigar Malanta, don haka yanzu shi ba Malami bane, ya zama odinari mutum kamar kowa. Don haka yadda yazo muna haka zamu mu'amalance shi.
Amma addinin Musulunci yayi umurni da cewa dole ne a girmama Malaman Allah da Annabi. Dole ne ayi masu da'a da biyayya. Dole ne a nuna masu kauna da soyayya. Dole ne a taimaka masu da abubuwan duniya, da 'yan kayan masarufi na rayuwa, domin su rayu, rayuwa ta mutunci. Saboda sun sadaukar da rayuwarsu wurin yiwa al'ummah hidima, don haka su ma ya zama wajibi ayi masu hidima.
An tambayi Abdullahi Ibn Mubarak:
"Su wanene mafifici a cikin mutane? Sai yace sune Malamai. Aka sake tambayarsa, wanene yafi a cikin sarakuna? Sai yace wanda yafi su tsoron Allah. Sai aka sake tambayarsa, wanene mafi kaskanci a cikin mutane? Sai yace, sune miyagun Malamai, wadanda suka sayar da addininsu aka biya su da duniyarsu." [Duba Mukhtar Al-Aghany, mujalladi na uku, shafi na 348]
Manzon Allah (SAW) yace:
"Halittun da suke cikin sammai da kassai, da kifi da yake a cikin ruwa, suna neman gafarar Allah wa Malami. Malamai sune magada Annabawa, Annabawa kuma basu bar gadon Zinari da Dirhami da kudade ba, abunda suka bari kawai shine ilimi; duk kuma wanda yayi riko da shi, to ya samu rabo mai yawa." [Abu Dawud, Tirmizi da Ibn Majah ne suka ruwaito shi]
Saboda muhimmancin Malami, an ruwaito cewa, a duk lokacin da Malami ya mutu, to addinin Musulunci ya samu tasgaro, har zuwa tashin alkiyama.
Allah Subhanahu wa Ta'ala yace:
"Allah yana daga darajar wadanda suka yi imani daga cikin ku, da wadanda aka ba wa ilimi daga cikin ku." [Suratul Mujadala, 11]
Kuma Allah Subhanahu wa Ta'ala yace:
"Kace, shin wadanda suka sani, wadanda aka ba wa ilimi, suna daidai da wadanda basu sani ba?" [Suratu Zumar, 9]
Annabi (SAW) yace:
"Wanda baya girmama manya baya tare da mu, wanda ba ya tausayawa na kasa baya tare da mu, wanda baya ba wa Malamai hakkinsu na girmamawa baya tare da mu." [Imam Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi, kuma Hadisin yazo a cikin Sahihul Jami'u]
Allah Subhanahu wa Ta'ala ya bamu labarin wani hamshakin Malami, wato Bal'am Dan Ba'ura; Malami, masani wanda duniya ta rude shi, ya biye wa son zuciyarsa, sai ya zama halakakke.
Allah Subhanahu wa Ta'ala yana cewa, game da labarin Bal'am Dan Ba'ura:
"(Ya Muhammad) Ka karanta masu, ka basu labarin mutumin da muka ba wa ayoyin mu (muka bashi ilimi), sai yayi watsi da su, sai shaidan ya biye masa, ya batar da shi, sai ya kasance daga cikin batattu. Da mun so da mun daga matsayinsa, da ilimin da muka bashi, to amma sai ya biye wa duniya da son zuciyarsa. Misalinsa kamar misalin kare ne, idan ka kore shi zai yi lallagi (ya fitar da harshensa waje), idan ma ka kyale shi zai yi. Wannan shine kwatankwacin misalin wadanda suka bijirewa ayoyin mu. Don haka ka basu labari, la'alla zasu yi tunani. Misalin wadanda suka karyata ayoyin mu ya munana, amma kawunansu suka kasance suna zalunta. Wanda Allah ya shiryar shine shiryayye, wanda kuma ya batar, wadannan sune hasararru." [Suratul A'araf, 7:175-178]
Bal'am Dan Ba'ura misali ne na waɗannan halaye na miyagun Malamai da na ambata.
Bal'am Dan Ba'ura yana daya daga cikin manyan malaman Bani Isra'ila, kuma ya rayu a daya daga cikin kauyukan kasar Sham (wato Syria a yau) a zamanin Annabi Musa (AS).
Bal'amu Dan Ba'ura ya kasance babban Malami, masani, yana yin harkar Malanta, kuma yana ba da labari game da abubuwan da zasu faru a nan gaba. Shi mabiyin addinin Ibrahim ne. Mutane sukan zo wurinsa yayi masu bayani game da su, da addu’a don albarkar dukiyoyinsu da rayuwarsu.
Bal'amu ya kasance na farko a cikin muminai kuma masani kan ilimomin Ubangiji, har Annabi Musa (AS) yayi amfani da shi a matsayin jigo mai karfi wurin yada addinin Allah. Matsayinsa da siffarsa ta kai matsayin da addu'arsa tana zama karbabbiya a wurin Allah.
Duk da irin wannan hali da matsayi da Allah yayi masa, ba zato ba tsammani sai kawai ya canza. Saboda son abun duniya da sha'awar abun hannun Fir'auna da kuma alkawurran da yayi masa na samun duniya. Kwatsam, sai ya kauce wa hanya madaidaiciya, kuma ya rasa dukkanin mutuncinsa da ikonsa na ruhi da na Ubangiji.
Da wannan sauyi, ba wai kawai ya nisantar da kansa daga hanya madaidaiciya ba, har ma ya zama daya daga cikin masu adawa da Annabi Musa (AS). Akwai kuma wasu dalilai masu karfi na karkatar da Bal'amu Dan Ba'ura yayi, kamar kokarin la'antar Banu Isra'ila, ya kai su ga fasadi da ridda ta hanyar mata, son duniya da kishin Annabi Musa (AS).
A cikin Alkur’ani mai girma, an ambaci labarin Bal’amu ba tare da suna ba; A cikin wannan labarin, an gabatar da wani mutum wanda ya kai wani matsayi mai muhimmanci da ayoyin Ubangiji da ilimi, amma son duniya da bin son zuciyarsa ya batar da shi.
Duk da cewa ba a ambaci sunan Bal'am Dan Ba’ura a cikin wadannan ayoyi ba, amma bisa ga wasu alamomi da kuma wasu Hadisai da fassarar malamai magabata, a cikin wannan ayar akwai alamun da za'a iya cewa wadannan ayoyin suna nuni ne zuwa ga wannan mutum, wato Bal'amu.
Watakila dalilin da yasa ba a ambaci sunan wannan mutum ba, kamar yadda Malamai suka bayyana, shine, a kowane zamani za'a iya samun irin wadannan miyagun Malamai, wadanda duk da ilimi da shiriya da Allah ya ba su, amma suke da karkacewa da raunin imani irin na Bal'am Dan Ba'ura.
Bayan wannan, ya kamata al'ummah su san da cewa, ba laifi bane Malamai suyi mu'amala da masu mulki, amma dai mu'amala ta gaskiya, ba ta ha'intar al'ummah ba.
Sannan, ya zama dole, tilas, kuma wajibi, muci gaba da yiwa kasarmu, da shugabanninmu da Malamanmu addu'o'i na samun nasara. Kar mu yarda mu zamo cikin masu zagi ko la'antar kasarmu da shugabanninmu da Malamanmu. Domin shiriyarsu, wallahi shine alkhairi a gare mu, lalacewersu kuma, wani karin sharri ne a gare mu.
Don haka babu abunda suke bukata a wurin mu a halin yanzu, illa addu'o'i da fatan alkhairi.
Allah ya taimake mu, yasa mu dace, amin.
Daga karshe, ina addu'a da rokon Allah Subhanahu wa Ta'ala ya shiryar da mu baki daya akan tafarki madaidaici, Allah ya shiryar da mu, da dukkanin Malamanmu da shugabanninmu, akan hanya madaidaiciya. Allah ya taimaki Malamanmu da shugabanninmu. Allah ka dora su akan hanya wadda ta ke ita ce daidai, amin.
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za'a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.