Bidiyon Tsiraici: Kotu ta yankwawa ɗan Masahawarci na musamman ga  Gwamna Tambuwal hukunci

Kotun Majistire ta ɗaya wadda alkali Shu'aibu Ahmad  ke jagoranta ta yankewa  Aminu Tafida ɗa ga Mai baiwa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal shawara kan saka hannun jari hukunci tare da wasu mutum biyu za su yi shekara huɗu da wata shidda kownensu a gudan gyaran hali.

Haka kuma ya ba su zabin biyan tara ta kudi dubu 400 kowanensu kan  bidiyon  'yar shekara 18 da suka watsa wanda sabawa dokoki ne.

Mutum biyu da suke tare da ɗan mashawarci ga Gwamna su ne Umar Abubakar da Mas'ud Abubakar Gidado.

Alkalin kotun Shu'aibu a lokacin da yake karanto hukunci ya ce kotu ta same su da laifi karara kan abin da suka aikata.

Alkalin ya ce laifin wanda ake tuhuma ya sabawa sashe na 171 a kundin dokar jihar Sakkwato kan haka  kotu ta ci su tarar dubu 200 kowanensu  ko zaman gidan gyaran hali na shekara biyu.

Haka kuma hukuncin yadawa da sayarda littafin tsiraici da hada baki wurin rashin gaskiya kotu ta yi masu tarar kudi dubu 50 rashin bayar da kudin dauri ne a gidan yari na shekara biyu. Haka sashe na 48 a kundin dokar jihar Sakkwato ya tanadi biyan dubu 50 ko zaman kaso na wata shidda ga wanda aka samu da laifin saba dokar.

Alkalin ya ci su tarar dubu 100 kowanensu hasafi ga wadda ta yi kara.

Wanda ya shigar da karar ASP Simon Sule da mai karar sun nuna gamsuwarsu da hukuncin da aka yanke, sun ce hakan zai zama tsoratarwa ga wasu.