Gwamnatin Katsina Za Ta Inganta Bangaren Lafiya, Ta Hanyar Daukar Ma'aikata 300

Gwamnatin Katsina Za Ta Inganta Bangaren Lafiya, Ta Hanyar Daukar Ma'aikata 300


Jihar Katsina - Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya amince da ɗaukar ma’aikatan lafiya 300. Gwamna Radda ya amince da ɗaukar ma'aikatan ne domin magance ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya na jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar Katsina, Musa Funtua, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch. 
Wannan mataki ya biyo bayan barazanar da ƙungiyar ma'aikatan jinya ta NANNM ta yi na janye ayyukanta daga ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro a jihar. 
Ƙungiyar ta yi barazanar ne sakamakon gazawar gwamnati wajen magance matsalolin tsaro da walwalar ma’aikatan lafiya. Kungiyar ta kuma yi barazanar shiga yajin aikin har sai baba ta gani idan har gwamnati ta gaza cika buƙatunta kafin ƙarshen yajin aikin gargaɗi na kwana biyu da za a fara a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, 2025. 
Janye ayyukan zai shafi ƙananan hukumomin da ke fama da rashin tsaro kamar su Batsari, Funtua, Malumfashi, Kankara, Kurfi, Danmusa, da Jibia. 
A cewar kwamishinan lafiyar, gwamnatin jihar ta gudanar da taron gaggawa tare da shugabannin ƙungiyar NANNM da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna buƙatun kungiyar. Kwamishinan ya bayyana cewa an cimma kaso 85% cikin 100% na yarjejeniyar da za ta warware matsalar. "Domin magance matsalar ƙarancin ma’aikata a fannin kiwon lafiya, Gwamna Dikko Umar Radda ya amince da ɗaukar sababbin ma’aikatan lafiya sama da 300."