Tuna Baya:Mawakan Sakkwato Sun Yi Fatar Sake Samun Gwamnati Kamar Ta Sanata Wamakko

Tuna Baya:Mawakan Sakkwato Sun Yi Fatar Sake Samun Gwamnati Kamar Ta Sanata Wamakko

 

Mawakan Sakkwato sun koka kan halin da suke ciki ganin yanda gwamnati mai ci ta yi halin ko'oho da su, wanda ma yake goyon bayan gwamnati ba a tsinana masa komai ba.

Mawaka musamman na baka da ake kira na gargajiya sun fara addu'a da fatar sake samun gwamnati kamar ta tsohon gwamna da ya gabata waton Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko.

 

Daya daga cikin mawakan da ya bukaci Managarciya ta sakaya sunansa ya ce gwamnatin Wamakko ta kula da su, ta mutunta basirarsu kan haka suka amfana kwarai dagaske sabanin yanzu da ba wani mawakin baka da ya samu wata kyauta ta shiga tsara saboda ya zuba basirarsa a wurin wake Gwamna ko Gwamnati.
 
Ya ce a baya ba da dadewa ba Sanata ya kira dukkan mawakan baka da ke tafiyarsa ya baiwa kowanensu  mota sabuwa dal a leda, suka bar gidansa cikin farinciki da murna bayan kyaututtuka kanana da yake yi masu a tsakaninsa da su.
 
MD Sokoto ya tuna baya ya ce "a lokacinka(Sanata Wamako) mun sha dadi har yanzu da mu ake damawa.

"Sanata Aliyu Wamakko yana kula da hakkin al'ummarsa dai-dai gwargwado, yara da manya na son jagorancin baba Alu nasara ce daga Allah,"  a cewar MD Sokoto.