Gwamna Buni ya nemi hadin kan yan adawa wajen gina jihar Yobe

Gwamna Buni ya nemi hadin kan yan adawa wajen gina jihar Yobe

Daga Muhammad Maitela, Damaturu.

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya yi kira na musamman ga yan adawa da suka fafata a zaben Gwamnan jihar su zo a hadu wuri guda ayi aiki tare domin gina jihar ta bunkasa.

Alhaji Mai Mala Buni ya yi wannan kira jim kadan bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ayyana shi a matsayin wanda ya samu nasarar zaben Gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar APC, a zaben ranar Asabar.

Ya kara da cewa, “Wannan nasara ce ta daukwacin al'ummar jihar Yobe, ba ni kadai ba."

“Saboda haka ina kira ga kowa da kowa ya zo mu hada hannu wuri guda domin ciyar da jiharmu ta Yobe gaba." In ji zababben Gwamnan.

Har wala yau, ya jaddada cewa wannan nasara za ta kara masa kwarin gwiwa kuma ta kara tabbatar da cewa gwamnatinsa ta taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaban jihar. 

“Wannan zabe karo na biyu shaida ce dangane da amincewar al'ummar jihar Yobe da suka nuna min, kuma zai kara mini karsashi wajen kara kwazo da himma wajen ci gaba da karin ayyukan ci gaba." Ya nanata. 

Bugu da kari, Gwamna Buni ya yaba tare da mika sakon godiya ga al'ummar jihar Yobe bisa amincewar da suka nuna masa wajen fitowa kwansu da kwarkwata su sake zabarsa karo na biyu.