Matasa A Kafafen Sada Zumunta: Cigaba da Ƙalubalen da suke Fuskanta

Matasa A Kafafen Sada Zumunta: Cigaba da Ƙalubalen da suke Fuskanta


Ruƙayya Ibrahim Lawal Sokoto.

Kafar sada zumunta dandula ne da matasa suke dandalewa tare da bajakolin fasahohinsu imma nagartattu ko ɓatattun fasahohi, kazalika wuri ne da matasa ke yin dandazo don yin hirarraki, musayar ra'ayi da yaɗa labarai, hotuna, bidiyo ko wasu abubuwa masu kama da hakan.

*Ire-iren Kafafen Sadar Da Zumunta Na Zamani*

* Fesbuk 
* TikTok 
* WhatsApp 
* YouTube 
* X (Twitter)
* Instagram 
* Thread da sauran su.

*Matasa a kafafen sada zumunta a yau*

Matasa a kafofin sada zumunta a yau sun zama abin da suka zama, sun rasa alƙibla guda ɗaya da suke fuskanta, sun ajiye hankulansu a gefe sun tsiri hauka da yin abin da ba shi kenan ba. Sun kasa fahimtar manufa ɗaya da suke so su cimma a dandalin, yau ka ga matashi a ƙarƙashin tutar wannan ra'ayin gobe ya canza zuwa wani.


*Tasirin Kafafen Sada zumunta ga rayuwar matasa.*


Tasirin kafofin sada zumunta ga matasa yana da ɓangarori biyu, yana bayar da damar fa'idantuwa da kuma ƙirƙirar manyan haɗurra. Duk da yake yana iya inganta dangantaka, ƙirƙire-ƙirƙire, da samun bayanai masu inganci har ma da akasinsu, yana kuma ingiza matasa ga cin zarafi ta yanar gizo, da ƙalubalen lafiyar ƙwaƙwalwa kamar damuwa da bakinciki. Idan matashi mai rangwamen hankali ko matsalar ƙwaƙwalwa yana leƙa kafafen zai iya cin karo da bayanan da za su iya ƙara taɓarɓare lafiyarsa idan sun tasirantu a zuciyarsa.

Wasu tasirin kafofin sada zumunta a kan matasa sun haɗa da sauye-sauye a cikin halayensu da ɗabi'unsu. Wasu daga cikin waɗannan sauye-sauyen na iya yin illa ga rayuwarmu, saboda abubuwa kamar matsin lamba daga abokai da kuma damuwar da ke tattare da shi, da buƙatar ci gaba da kula da martabar kai a shafukan sada zumunta.


*Taya  kafar sada zumunta ke sauyawa matasa ɗabi'u?*


° *Tasirantuwar al'adun ƙetare:* matasa suna kallon rayuwar da ake gudanarwa a ƙasashen ƙetare, yanayin suturunsu maganganunsu da al'adunsu. Wannan ya taimaka sosai wurin saƙawa matasa ƙaunar waɗancan rukunin mutanen da kwaikwayon ɗabi'unsu, salon maganarsu da saka suturu irin nasu. 

°  *Neman shahara:* Da yawan matasa sun fi mayar da hankali kan neman shahara ta kowanne irin yanayi fiye da ɗabbaƙa ɗabi'u da tarbiyyar da suka samo daga tushe.

°  *Chanjin Hulɗa:* Ma fi yawan matasa a yanzu sun fi mayar da hankali a kan hirarraki a kafar sadarwa fiye da hira a cikin gungun mutane a zahiri. Rayuwar wasu daga ciki kaso 80 bisa 100 ta koma a kan kafafen sadarwa.

° *Wayewa da ilmantuwa:* Matasa suna ƙara samun gogewa a fannin ilimi, samun horo na musamman da sabbin dabaru na aiwatar da wani abu da zai taimaki rayuwarsu ta gaba.

° * Ƙarancin Nutsuwa:* Ta'allaka kaso mai yawa na rayuwa zuwa ga kafafen sadarwa kan haifar da ƙarancin Nutsuwa, ƙarancin lokacin karatu, aikin gida, kula da tarbiyyar yara, rashin mayar da hankali ga aikin da ke gaban mutum. Yawancin matasa sukan iya kai har talatainin dare suna hira a midiya wanda hakan kan shafi har ibadarsu ma.

*Ruɗanin matasa a kafafen sadarwa*


Wasu daga cikin matasa masu bibiyar dandulan sada zumunta sukan shiga ruɗani da rashin fahimtar huɗubar da za su kama. A waɗannan kafafen ne za ka samu abubuwa kamar haka:

  - matashin da bai taɓa zuwa makaranta ba yana koyar da cikakkun horarrun ɗalibai yadda za su gudanar da rayuwa.
  -  Matashiyar da ba ta taɓa aure ba tana koyar da matan aure yadda ake zamantakewar aure da tattalin miji.
  -  Baƙauye yana koyar da ɗan birni yadda za yi rayuwa a waye.
  -  Jahili yana wa'azi, malami kuma yana aikata aikin jahilci.
  -  Matashi yana horar da matasa a kan illar abin da yake kan aikatawa bai daina ba.
  -  Matashi yana tsoma baki a matsalar da shi kansa yana da ita, sai kuma a hange shi yana zagin wanda ke cikinta.

*Me yakamata matasa su yi don kaucewa haɗɗuran kafafen sada zumunta*


1 Don kare kansu daga haɗarin kafofin sada zumunta, yakamata matasa su ba da fifiko ga saitunan sirri, su guji raba bayanan sirri, kuma su yi taka tsantsan game da waɗan da suke hulɗa da su kan layi. Ƙirƙirar iyakoki, sadarwa a fili tare da amintattun manya da haɓaka ƙwarewar karatun dijital mai ƙarfi su ma suna da mahimmanci. 

2 Idan kuna kokawa da jarabar kafofin watsa labarun, cin zarafi ta yanar gizo, ko wasu batutuwan kan layi, kada ku yi shakkar neman taimako daga amintaccen babba ko ƙwararru. Ku ƙarfafa halaye masu kyau a can, haɓaka kirki kuma zama ɗan ƙasa nagari.

3 *Kare Bayanin Keɓaɓɓancewarka*: Bincika akai-akai ka kuma daidaita saitunan keɓantawa a kan dandamalin kafofin sadarwar don sarrafa wanda zai iya ganin abubuwan da kuka aika/wallafa, ko wanda za ku ga abin da ya wallafa.

4 Yi hankali da mu'amalar Intanet: Kar a karɓi buƙatun abokai ko bi buƙatun mutanen da ba ku sani ba. Ba da rahoton ayyukan da ake tuhuma, toshe su kuma ka ba da rahoton masu amfani da kafafen waɗanda ka lura suna yin abubuwa na rashin dacewa.


*Manazarta*


Google Search. (n.d.-c). https://www.google.com/search?q=youth+on+social+media&oq=&gs_lcrp=EgZjaHJvbWUqDAgFECMYJxjqAhiLBDIGCAAQRRg6MgcIARBFGLABMgkIAhAFGEIYwwMyDAgDECMYJxjqAhiLBDIMCAQQIxgnGOoCGIsEMgwIBRAjGCcY6gIYiwQyDAgGECMYJxjqAhiLBDIMCAcQIxgnGOoCGIsEMgwICBAjGCcY6gIYiwQyDAgJECMYJxjqAhiLBDIMCAoQIxgnGOoCGIsEMgwICxAjGCcY6gIYiwQyDAgMEC4YJxjqAhiLBDIMCA0QIxgnGOoCGIsEMgwIDhAjGCcY6gIYiwTSAQYtMWowajSoAg6wAgHxBSFHGBz3is4K&client=ms-android-transsion&sourceid=chrome-mobile&ie=UTF-8


Google Search. (n.d.-b). https://www.google.com/search?q=what+should+youth+suppose+to+do+to+protect+their+self+for+social+media+risk&oq=what+should+youth+suppose+to+do+to+protect+their+self+for+social+media+risk&gs_lcrp=EgZjaHJvbWUyBggAEEUYOTIHCAEQIRiPAtIBCTYwNTcyajBqNKgCAbACAQ&client=ms-android-transsion&sourceid=chrome-mobile&ie=UTF-8