Gwamnatin Kano Ta ƙara Sassauta dokar hana fita daga 6 na safe zuwa 6 ba yamma

Gwamnatin Kano Ta ƙara Sassauta dokar hana fita daga 6 na safe zuwa 6 ba yamma

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano .

Gwamnatin jihar Kano ta daɗa sassauta dokar hana Zirga-zirgar da ta sanya a faɗin jihar.

Kwamishinan 'yansandan jihar CP Salman Dogo Garba ne ya sanar da hakan a yayin zantawar sa da manema labarai a fadar gwamnatin Kano, jim kaɗan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki a fannin tsaron, da Gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusif ya jagoranta.

CP Dogo ya ƙara da cewa Gwamnatin Kano ta bada damar ne domin al'ummar su ci-gaba da fita harkokin su na yau da kullum.

A ƙarshe sanarwar tayi fatan al'umma za su bi wannan doka domin tabbatar da zaman lafiya a lungu da saƙo dama ƙaruwar ci-gaban jihar.

Gwamnatin jihar Kano dai ta sanya dokar hana fitar ne da yammacin ranar Alhamis ɗin da ta gabata, bayan zanga-zangar matsin rayuwa ta rikiɗe zuwa fasa shagunan ƴan Kasuwa ana deɓewa da kuma kwashe kadarorin Gwamnatin.