Sojoji sun kashe babban na hannun daman Turji, Kallamu, a wani samame da suka kai a Sokoto
Dakarun Runduna ta 8 na Sojojin Najeriya sun hallaka fitaccen jagoran ’yanbindiga, Kachalla Kallamu, a wani samamen hadin gwiwa da suka kaddamar a karamar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.
Wata majiyar soja , wadda ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Talata, ta bayyana samamen a matsayin “babban rauni ga cibiyar Turji,” tana mai cewa Kallamu na matsayin babban na hannun daman shugaban ’yanbindiga da ake nema, Bello Turji.
A cewar majiyar, an kashe Kallamu tare da daya daga cikin manyan masu samar wa Turji kayayyakin aiki a lokacin wani samame da safe a kauyen Kurawa ranar Litinin.
Majiyar ta kara da cewa an gudanar da aikin ne da muhimmiyar gudunmuwar kungiyoyin sa kai na yankin.
“Mun dade muna bibiyar Kallamu. Kashe shi wata babbar nasara ce wajen raunana garkuwar ’yan bindigar da ke Sabon Birni da kewaye,” in ji majiyar.
Mamacin, wanda asalin dan Garin-Idi ne a Sabon Birni, ya dade yana addabar al’ummar yankin. Ana zargin ya gudu zuwa jihar Kogi bayan ya tsere wa luguden soji a watan Yunin 2025, amma ya sake shigowa Sokoto kwanan nan ba tare da an sani ba.
Majiyar ta yaba da karin bayanan sirri da ake samu daga al’ummomin yankin, tana mai cewa hadin kai tsakanin mazauna Yankin da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarorin baya-bayan nan.
Jaridar Tribune ta rawaito cewa an ci gaba da murnar labarin a Sabon Birni, yayin da mashawarci na musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (Rtd.), ya yaba wa dakarun bisa “cigaba da jajircewa da kwararru” wajen yaki da ’yan bindiga.
managarciya