Ina Goyon Bayan Shugaba Buhari Ya Cigaba Da Yakar Macutan Kasar Nan----Walin Kalgo

To amma me zaisa abari wasu mutanen banza 'yan tasha su rika ruruta wuta tsakanin wadannan kungiyoyi guda biyu har ta kai ana zage-zage da kone-kone da farfasa gidaje da ofisoshi da motoci; misali ka duba irin muhimman mutane masu darajja a Jihar Kebbi takai suna yiwa junansu maganganu maras dadi, naji yadda Sani Zauro Zannan Gwandu ya yi wa Sani Dododo da kuma yadda Sani Dododo yake maida wa wani dan Argungu martani a cikin kafafen yada labarai, irin wadannan maganganu na banza bai kamata dattijai suna irin wa]annan maganganu ba, amma idan kai da mutum ne ka zage shi da sauke-sauke amma ka fito cikin kafafen ya]a labarai kana zage-zage a matsayinka na dattijo bai dace ba, ka karantar dana bayanka kenan kuma ka haddasa fitina, har zuwa ga yan’uwa da abokan arziki, wanda ba’a san ranar }arewar ta ba, saboda siyasa.

 Ina Goyon Bayan Shugaba Buhari Ya Cigaba Da Yakar Macutan Kasar Nan----Walin Kalgo

 

Malam Abubakar Muhammad Atiku Walin Kalgo shi ne tsohon limamin sojojin Najeriya, yana daya daga cikin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kebbi Da kuma kasa baki daya. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce duk da rigingimun da jam’iyyar APC ta ke fuskanta, jam’iyyar ba za ta wargaje ba.

Managarciya: Me za ka ce game da kafa kungiyoyin siyasa da aka yi a Jihar Kebbi BBSO da 4+4?

Walin Kalgo: Bismillahir Rahmanir Rahim, a matsayina na almajiri na addinin musulunci kuma mai sha’awar siyasa saboda Muhammadu Buhari dattijo nake jam’iyyar APC a Jihar Kebbi, to lokacin da aka yi (two terms) idan ba’a manta ba, lokacin tsohon Gwamna Saidu [akingari, Allah ya sani Saidu ya sani yana nan da ransa a yanzu da muke maganar da kai, na sami Saidu gaga ni sai shi, sai Allah na fa]a masa a matsayinka na Gwamna uban kowa kana gani yaran nan sun fito da wani abu wanda zai kawo maka mastala, a cikin siyasa a samu baraka, saboda haka ka kirasu ka yi musu alheri kuma ka yi godiya ka ce musu su bari, har sai in manyan ‘yan siyasa sun ha]u sun tattauna akan kafa kungiyoyin siyasa. Amma Saidu bai yi amfani da Magana ta ba, kuma na yi wa shugaban jam’iyyar PDP na wancan lokacin Marigayi Alhaji Kasimu Baura magana na ce ya kuka bari ana ta bude ofisoshi na kungiyoyin siyasa barkatai. Irin bude wadannan ofisoshi ba zai haifar manu da da mai ido ba, akan irin wannan ne har yanzu a Jihar kebbi muke da bangaranci a cikin siyasarmu, domin alokacin Saidu bai yi amfani da shawarwarin da muka ba shi ba.

Bari in koma ga tambayar da ka fara yi mani, a halin gaskiya su wadannan kungiyoyi na siyasa da aka kafa anan Jihar Kebbi BBSO da 4+4 ba alheri ba ne, ga maigirma Gwamna Bagudu, na sha zuwa domin in fada masa illolin kafa waannan kungiyoyin siyasa amma Allah bai sa mun sadu da shi ba, na fada ma na kusa da shi, su fada masa illolin kafa wadannan kungiyoyin siyasa domin dukkansu wadanda suka kafa kungiyoyin mutanen ne na kusa da Gwamna kuma duk bukatar su guda ce nasarar Buhari da Bagudu a zaben 2019 idan Allah ya kaimu.

To amma me zaisa abari wasu mutanen banza 'yan tasha su rika ruruta wuta tsakanin wadannan kungiyoyi guda biyu har ta kai ana zage-zage da kone-kone da farfasa gidaje da ofisoshi da motoci; misali ka duba irin muhimman mutane masu darajja a Jihar Kebbi takai suna yiwa junansu maganganu maras dadi, naji yadda Sani Zauro Zannan Gwandu ya yi wa Sani Dododo da kuma yadda Sani Dododo yake maida wa wani dan Argungu martani a cikin kafafen yada labarai, irin wadannan maganganu na banza bai kamata dattijai suna irin wa]annan maganganu ba, amma idan kai da mutum ne ka zage shi da sauke-sauke amma ka fito cikin kafafen ya]a labarai kana zage-zage a matsayinka na dattijo bai dace ba, ka karantar dana bayanka kenan kuma ka haddasa fitina, har zuwa ga yan’uwa da abokan arziki, wanda ba’a san ranar }arewar ta ba, saboda siyasa.

Managarciya : Me zaka ce game da maganganun da mai ba Gwamna shawara ta harkar siyasa Alhaji Yusuf Rashid yayi akan Faruk Yaro Enabo P.A, wajen babban taron 4+4.

Walin Kalgo: To a halin gaskiya mai ilimi kamarsa kuma ]an sarki wanda ya fito daga babban gida kuma jikan Abdullahin Gwandu, wanda yana iya ri}e wannan gida a halin da muke ciki yanzu. Gaskiya irin wa]annan maganganu da ya yi a wurin wannan babban taro da aka gudanar ba halinsa ba ne, ko shi yanzu da ya yi wa]annan maganganu idan ya tuna da abinda ya fa]a zai ce ya yi ba}in cikin fa]in su. Saboda haka muna kira gareshi nan gaba irin wa]annan maganganu bai kamata su ri}a fitowa daga bakin sa ba, kuma kada wasu ‘yan siyasa su goyi bayan wa]annan maganganu da ya yi, ya tuna fa duk dan }asar Gwandu talakkan shi ne, in ]an Sarkin Gwandu ko Jikan  Sarkin Gwandu ya ce baya son wani talakkan }asar Gwandu to ya yi kuskure.

Ina kuma kira ga mu malammai idan muka zo yin wa’azi mu ri}a fa]in kalamai masu amfani ga jama’a ba irin kalamai da za su jawo tashin hankali ba, mu guji haddasa fitina tsakanin ‘yan siyasa dan biyan wata bu}atarmu.

Managarciya : Me zaka ce game da korafe-korafen da al’ummar yankin Zuru da Yauri ke yi cewa an barsu abaya musamman wajen na]a mukamai?

Walin Kalgo: su masu  irin wa]annan }orafe-}orafe sun manta da cewa Gwandu ita ce uwa ga yankunan nan guda uku, kuma a sarautun nan guda uku Argungu da Yauri da Zuru, Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Kebbi shi ne Maimartaba Sarkin Gwandu, idan aka ce kai shugaba ne, to kai ne uba kamar Abuja ne da sauran Jihohin Nijeriya, mu dai abin da muke bu}ata duk daga inda ka fito in dai ]an Jihar Kebbi kake to ka nuna halin }warai a wurin gudanar da aiyukanka kuma ka yi adalci ga kowa ga duk inda mutum ya fito ko Argungu ko Yauri ko Zuru ko Gwandu.

Mu}ami yana da kyau ga duk wanda ya dace a ba shi ko da kafiri ne, indai zai yi adalci akan kowa ya halatta a ba shi mu}amin, in dai har ya iya aikin kuma in zai ba kowa ha}}insa ana iya ba shi domin musulunci ya yarda, amma mutane abin da ya dame mu shi ne hassada, amma ya za’ace wanda bai cancanci ya ri}e mu}ami ba a ba shi, irin wannan ba zai haifar mana da ]a mai ido ba, saboda haka ina kira ga yan’siyasar Jihar Kebbi mu ba da ha]in kai dan ciyar da Jiharmu gaba domin shi ne mafita ba wai yin }orafe-}orafe akan mu}ami ba.

Managarciya : To yanzu menene mafita?

Walin Kalgo: Madalla, ga mafita nan,  Sanata Muhammadu Adamu Aliero da Gwamna Bagudu sun zauna sun yi nazari cewa idan abin da ke faruwa ya ci gaba a cikin wa]annan }ungiyoyi to jam’iyyar APC za ta samu matsala kuma za’a samu fitintinnu a cikin al’umma saboda haka Sanata Adamu Aliero ya kira taron manema labarai ya ba da sanrwar rushe duk wata }ungiyar siyasa wadda aka kafa ta a }arkashin jam’iyyar APC, ya ce kuma duk wata }ungiyar siyasa wadda aka }ir}iro ta a cikin APC yanzu ta koma a matsayin }ungiyar ya}in cin za~e na jam’iyyar APC, duk sun koma cikin }ungiya guda kenan.

Managarciya: Wace shawara za ka ba shugaban }asa Muhammadu Buhari?

Walin Kalgo: Shawarar da zan ba shugaban }asa Buhari ita ce, ya ci gaba da wannan aiki na ya}i da mahandama da macuta da suka sace mana ku]inmu suka kai wa iyayen gidajen su a kasashen waje. Ina }ara kira ga shugaban }asa duk girman mutum ko mu}aminsa ko shi wanene idan ya ci ku]in al’umma a tursasa ya dawo da su kuma a hukunta shi, su kuma al}alai su ji tsoron Allah su tuna za su koma gaban Allah, ko kai musulmi ne ko kirista za ka mutu, saboda haka muna nan muna ta addu’a duk wanda ya ]aure wa azzalumi gida Allah ya tona asirin shi.

Don haka Buhari ya ci gaba da aiki, Allah zai kare shi daga dukkan miyagu, duk masu }ulle-}ulle ba za su samu nasara ba. Ni ba ma’aikacin Gwamnati ba ne, kuma ba na yi mata kwangila, amma ina son a samu gyara a kasar nan. Gwamnonin APC kuma su ji tsoron Allah su taimakawa shugaban }asa ta fannin tsaro da kuma kama ~arayin da suka sama da fa]i da ku]in a’lumma, kuma su fito da shirye-shirye na inganta harkokin al’ummar Jihohinsu.

Managarciya : Me zaka ce ga jama’ar kasa?

Walin Kalgo: Jama’ar }asa su tuna bayan wuya sai da]i, kuma bayan ba}in ciki sai farin ciki idan muka tuna a lokacin mulkin Buhari na soja a baya, mun sha wahala a farko, bayan haka ka]an komai ya zo ya daidaita, da]i ya zo. Sai daga baya aka kawar da shi aka zo aka mayar da hannun agogo baya, aka ciwo mana ba shi duk da munce bamu so, aka karya mana darajar kudi aka mayar damu bayi. Ga yadda muka iske kanmu a ciki yanzu ta yadda komai ya ta~ar~are a }asar nan.

Bashir Lawal Zakka, Birnin Kebbi.