ANA BARIN HALAL....:Fita Ta 50

ANA BARIN HALAL....:Fita Ta 50

ANA BARIN HALAL....:

*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE* 

*®️GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_(Gaskiya Dokin Ƙarfe

Burin Mu Faɗakar Da Al’umma Domin Ribatar Duniya Da Lahira.)_

*BISMILLAHI RAHMANIR- RAHIM*

Idan kana/kina sha’awar:

_**Updates akan tallafin gwamnati (Grant & Loan)._

_**Hanyoyin samun kuɗi ta kasuwanci na online._

_**Sana’ar hannu da za ki iya yi daga gida._

_**Dabarun amfani da waya wajen samun kuɗi._

_To wannan group ɗin na Business/Grant/Loan naku ne! Zaku samu labarai kai tsaye + shawarwari masu amfani in sha Allah._
Join yanzu don kada ku rasa sabbin damarmaki*
https://chat.whatsapp.com/C64wC3IDhW6FtwjSpWWDiL?mode=ac_t

*Page 50*


*INA UWARGIDAYEN SUKE? NACE INA UWARGIDAYE MASU CAPACITY SUKE, IDAN BAKI YI MATSA GA MASU* *AUTHOURITY, NACE TSAYA IDAN BAKIYI GA AMARE MASU AUTHOURITY,* *IDAN KIN SHIRYAH GWANGWAJE SHINFIƊAR MAIGIDA,* *TOU KI ƘYALE  ƳAN LOCALLITY KI MATSO KI SAYI NAKI,* *BEDSHEETS ƳAN GASKE, KU MATSO KU YAƘI PORVERTY DAGA TASKAR HALIMA YISUF GWARZO, INA MAI TABBATAR MIKI IDAN KIN SHIMFIƊA ZAKI ZAMA MAI CAPACITY MAI AUTHOURITY,* *DOMIN KI WANKE ZUCIYAR MAIGIDA YA HASKAKA,*
*MUNA AIKAWA DA SHI KO'INA A FAƊIN ƘASAR NAN.*
*DOMIN SAYEN ƊAYA KO SARI, KU TUNTUƁE NI TA WANNAN LAMBAR*
08064586559


~_________~
Bamu muka farka ba sai da hasken rana ya hasko idon mu, a firgice A.G ya farka, salati naji yanayi na buɗe idona da wuri,   "Eeshaa wani irin bacci kenan mukayi haka? Har gari fa ya waye rana ya fito,",  ƙarasa faɗa yayi yana shigewa toilet ɗin ɗakina, tashi nayi zaune cike da mamakin irin baccin da mukayi, nifa daga cewa bari na ɗan kwanta kaɗan kafin ya tashi shikenan sai da gari ya waye tangararan tukun muka farka?.

Yana fitowa na shige da sauri nayi wanka da brush, bayan na fito ne naga baya ɗakin, amma ga sallaya a shimfiɗe alaman anan yayi sallan, shiryawa nayi na fice zuwa kitchen, ina cikin aiki ya shigo, rungumo ni yayi ta baya,  fuskan shi ya ɗaura a kafaɗa na, har ina jin hucin numfashin shi, murya chan ƙasa yace,  "Beauty jiya kawai sai nayi bacci, wani bacci mai shegen daɗi, nayi mamakin baccin danayi baby",   murmushi nayi ban ba shi amsa ba, haka dai na ƙara aikin nan yana manne da ni, bayan munyi breakfast ne ya sake tambayana  naga wani chanji danake shan maganin? Girgiza kai nayi alaman babu wani chanji,   "inaga dai kawai a nemi maganin gargajiyan aga ko zai tsaya, ni wallahi tsoro nakeji kada jininki ya ƙare",   ya faɗa duk fuskan shi cike da damuwa,  nima dai abun yana damuna, amma  na ƙarfafa mishi guiwa akan insha Allahu za'a samu sauƙi, wunin ranan dai haka muka ƙare shi rungume da juna, ana sallan magrib Alhaji Inuwa kakanshi ya ƙira shi akan ya taho tare da ni yana neman mu, hijab na saka muka wuce gidan.


Muna isa gidan muka samu mummy agidan suna tare da Dadda a parlon Daddan,,  gaishe su mukayi dukkan mu, nidai ina zaune a ƙasan carpet na lanƙwasa ƙafafuna duka, hiran jinya na naji sunayi da A.G da mummy wa Daddah, ita ashe sai yau taji da mummy ta ƙira da safe ta gaya musu, akan ko za'a sama mana mai maganin gargajiya ko na islamic,  shine Alhaji Inuwa ya ringa faɗan meyasa ba'a sanar musu da wuri ba? An bar yara suna ta fama da damuwa, yanzu mai maganin ne yazo shine aka ƙiramu, nidai tunda naji sunce mai maganin yazo naji hankalina ya tashi, wani tsoro ma duk sai ya rufe ni, kadafa aje ina da wani matsala ne tuntuntuni.

A parlon A.G ya barmu ya wuce wurin Alhaji,  nidai kaina yana sunkuye a ƙasa ina wasa da yatsuna, sukuma suna ta hiran su kaman uwa da ƴar'ta, duk sun ban sha'awa kaman ba surukune ba.

Alhaji inuwa ne ya ƙira wayan Dadda yace muzo parlon shi dukkanmu,  da ƙyar na miƙe ƙafana na bi bayan su, duk inda ƙofa yake ajikina zufa yana fitowa, cike da tsoro da wani fargaba da ban san daga ina yake ba suka runtumo mun,  a haka dai na cigaba da jan ƙafana har parlon Alhaji,  da sallama a bakina na shiga parlon, su huɗu muka same su a zaune a parlon, Alhaji, A.G, sai wani dattijon mutum kan shi da rawani sai jikin shi da Alkyabbah, sai gefen shi kuma wani matashin dattijo ne, wanda a ƙallah zai iya kai shekaru hamsin,  nan ma ƙasa na nema ta gefen mummy na zauna, itama mummyn a ƙasa kan carpet take zaune, A.G na a ƙasan naga ya zauna, Daddah ce kawai ta zauna akan kujera kusa da Alhaji, gashe da Alhaji nayi ya amsa mun fuskan shi cike da murmushi, ga annurin dattaku a fuskan shi,  mayar da kaina nayi kan wannan Dattijo mai rawani aka nayi, sai naga shima gaba ɗaya fuskan shi a kaina, gaba nane yayi mummunan faɗuwa, saboda haka nayi saurin sauƙe idona ƙasa,  murmushi yayi ya maida kanshi kan Alhaji yace,  "naji dukkan bayanan ka Ahaji, amma kuma ko ma aljanine ya ke sakata haka tou aljanine na ture, domin daga shigowan ta naga inuwan shi yana mara mata baya, amma insha Allahu komai zai daidaitu",   ɗago kaina nayi da sauri na dubi A.G da mukaji muryan shi yace,  "Aljani kuma Ranka ya daɗe"?  A firgice yayi maganan, daga dukkan alamu abun ya bashi tsoro, murmushi dattijon yayi bai bashi amsa ba, Alhaji kuma sai ɗaga kai yakeyi kawai, daga nan alaramman mutumin ya ƙira sunana  "AYSHAA",  ɗago kaina nayi ban iya amsawa ba, sai idona danaji suna cikowa da hawaye,  alama ya mun dana taso naje gaban shi,  ban tashi ba sai idona dana mayar kan A.G, shima kallona yake duk hankalin shi a tashe,  Alhaji ne ya sake ƙirana da nazo gaban wannan dattijon, babu yadda na iya ne kawai ya sakani ƙarasawa gaban mutumin, kuma kada kiyi tunanin da ƙafana naje gaban shin,  a'a samun kaina nayi da ja da gindi har na ƙarasa gaban shi,  miƙawa matashin dattijon hannu yayi akan ya miƙo mishi jakan da yake gefen shi,  

Tambaya ya fara mun game da ire-iren mafarkan da nakeyi, da kuma yadda jinin yake zuwa, akan da yawa ne ko kaɗan,?  Buɗe baki nayi zan mishi bayani amma naji kaman an naɗe harce na, juyawa nayi da sauri na dubi A.G ko shi zaiyi mishi bayani, amma shima sai naga alaman jira yake yaji mai zance,  juyowa nayi zan dubi mutumin kawai naji ya saka mun wani roban faro da yake ɗauki da wani ruwan abu kaman ruwan nono, fari mai ɗan kauri, amma azaban abun a hancina kaman an fasa mun bom a tsakar kaina, haka naji zafi da ƙarfin abun acikin kaina, nidai abunda zan iya tunawa shine naji na yi ihuu iya ƙarfina, sannan na miƙe zan tashi naji muryan mutumin yana umurtan A.G daya riƙeni, daga nan ban san meya faru ba, sai wuraren ƙarfe tara na dare na farka na ganni rungume a jikin A.G,  mummy na riƙe da hannayena, Dadda kuma tana zaune a gefen mummy hankali duk a tashe, gefe ɗaya kuma Alhaji ne zaune da waƴannan mutanen,  farkawa na ne naji mutumin na hamdalah, sannan ya miƙe tsaye shida abokin tafiyan shi, sallama yakeyiwa Alhaji akan gobe idan Allah ya kaimu da safe ɗayan zaizo, ka duk yadda ake ciki su neme shi, haka Alhaji ya miƙe domin ya musu rakiya,   A.G daga inda yake zaune rungume dani ya ke yiwa mutanen sallama,  godiya sosai naji su mummy da Dadda suna musu, a haka suka fice tare da Alhaji,  tambaya na mummy tayi zan iya tashi mu wuce ɗaki?  Juya kaina nayi gefe, da ƙyar na iya buɗe bakina nace,   "mummy bana jin ƙafana a jikina",   ido ta mayar kan ƙafana a ɗan tsorace tace,  "doug ga ƙafan ki, ko kina jin suma miki ciwo ne"?  Lumshe ido nayi ban sake magana ba, daga nan naji A.G ya saɓeni kawai yayi hanyar ɗakin Hajiya daddah da ni,  lumshe idonayi saboda wani irin ƙunci da nakeji a cikin zuciyata, a haka yaje ya kwantar da ni a ɗakin kan gadon Daddah,  zama yayi a gefe na yana tambayan abun da nake so?  Nidai a cikin zuciyata bana jin ina son tankawa kowa magana, haka yayi ya gajji ya barni,  Dadda ce tazo ta zauna a gefena ta ƙira sunana, ɗago kaina nayi na kalleta,  ganin ina kallonta yasa ta tambayeni me nake son ci takawo mun?  Ƙura mata ido nayi ban ce uffan ba, saboda wani iri nakeji a cikin jikina da kaina, dukkansu ukun babu yadda basuyi dani ba amma ban tanka suba, haka suka gajji kowa ya koma gefe ya zabga uban tagumi.


Washe gari da safe mutumin nan yazo, wuraren ƙarfe 11:00am yazo, Hajiya ummah kuma da Aunty rakiya tun wuraren ƙarfe 10:00am suka iso, saboda duk yadda akayi mummy ta ƙira ummie ta sanar mata, shiyasa sukayi smmakon zuwa dubani, suma babu yadda basuyi dani na amsa musu magana ba amma fir naƙi, domin wani mummunan ƙunci nakeji a zuciyata, ji nake idan na buɗe baki nayi magana zuciyata zata fashe, 
Wanka Aunty Rakiya ta sakani na tashi mukaje tare da ita ta tsaya nayi, sannan ta bani wani roba da akasaka ruwan magani kuma naga an zuba wani turare mai ƙamshi a ciki wai nayi wankan da shi bayan nagama normal wanka na, haka dai badon rai yaso ba na karɓa nayi wankan, zani aka bani na ɗaura muka fito,  kaskon wuta naga Dadda ta miƙo wa Aunty rakiya, sannan suka koma parlor suka barmu, wani garin magani ta zuba akan kaskon sannan ta sakani na tsuguna akai, bayan na gama ta saka na tashi ta bani pant data manna mishi pad a jiki na saka, nayi tunanin maina zan shafa, amma sai naga labarin ya chana, wani maganine daga gani mayukan islamic ne aka haɗa ta miƙo mun, hattah gashin kaina sai da na shafa mish, ina gamawa ta bani wata doguwar riga mai haɗe da gyalanta nasaka, duk yadda naso shafa turarena ta hanani, 

 lokacin da mutumin nan ne yazo  jikina ya sake burkicewa, don maganin daya shigo da shi akan dole sai na shanye a lokacin ne ya tayar mun da hankali,  wanda har sai da na ringa zabga mishi ihuu ina kuka yadda naso,  A.G dai sai lallaɓani yake har saida nasha maganin, da ƙyar nasha, sannan ya bada wani magani akan na shafa ajikina sai nayi hayaƙi, aiko da daru da komai sai da nayi, bayan ya tafi ne naji yadda jiya aka ƙare da ni, lokacin mummy keyiwa su Hajiya ummah da Aunty rakiya bayani, hajiya ummah sai zabga salati kawai takeyi, "jiya kam ai munga tashin hankali, ae mutumin yana shaƙa mata maganin ta miƙe a firgece zata gudu, shine ya saka mijinta ya riƙota, nan kuwa suka fara bayani a jikin ta,  wai su biyansu akayi da jinin baƙin taure, baƙin agwagwa, baƙin kaza, baƙin yadi, baƙin zare, da tsiren gidan mashaya, kuma wai a hakan ma bai samu daman ƙarasawa jikinta ba, raɓanta yayi,"  mummy na musu bayani hajiya ummah ta sake zabga wani dogon salati tana kama haɓa, Aunty Rakiya ƙurawa mummy ido tayi, chan ta tambayi mummy   "tou basu faɗi waya sayo su ba"?  Mummy tayi ajiyan zuciya tace,  "cewa sukayi wai wata mata ce baƙa mai ɗan jiki guntuwa,  amma sunƙi faɗin sunanta, sun daice wai ta daɗe tana jefawa Ayshann sharruka basu kamata ne, wannan ma sunce tayi wasa da ibadunta ne da zama babu alwala yasa suka sameta,"    "ehhh babu shakkah zatona ya zama gaskiya, tabbas babu baƙa gajeruwa mummuna kaf a wanda na sansu sai Hauwa, kuma zatayi abunda yafi haka indai zuciyar da yake tare da Hauwa yana nan a ƙirjinta Usamanu bai taimaka an kaita ƙasar indiya a cire ba, don tabbas idan ba'a cire ba Hauwa zata kashe mutum idan ta samu sarari,"  hajiya ummah ta faɗa tana fashewa da kuka,  ido Dadda ta ƙura mata na wani lokaci, kafin daga baya tace,  "hajiya wacece hauwa? Akwai wacce kuke tunani zatayi wa Ayshaa irin wannan muguntan ne"?  Ajiyan zuciya Aunty rakiya ta sauƙe sannan ta dubi Dadda tace,  "matar babanta ce,"  sannan ta ɗaura da basu labarin abunda ya faru lokacin auren habiba, da wasu halaye na rayuwar mamie tunda aka aurota,  ita dai hajiya ummah kukanta sosai tasha, haƙuri suka ringa bata, chan bayan tayi shiru sai ta maida kallonta kaina tace,   "ni tsoron da nakeji ɗaya ne,  dubi yadda baiwar Allah yarinya ƙarama take fama da sharrin kishiyar uwa ba nata kishiyar ba, dubi yadda Ayshaa tayi jigum taƙi tankawa kowa, tsoro na kada shegen aljanin ya taɓa mata saitin kanta, miji yaje ya gaji yace ya fasa aure, ha yaro sam barka da shi,"  sai kuma ta sake fashewa da kuka tana tsinewa mamie da zuriyarta kaff,  haƙuri sukai ta bata, nidai ban san tafiyan su ba saboda baccin daya ɗauke ni, lokacin dana farka sai na samu sun tafi, A.G ma baya nan ya fita, daga ni sai Daddah, domin mummy ma wai ta tafi chan nata gidan, amma wai zata dawo jimawa.


Ranan monday jirgin safe A.G yabi ya koma Abuja, amma kafin ya tafi mun ɗan taɓa hira da shi sosai, don na ɗanji sauƙin ƙuncin da nakeji, lokacin da Alhaji ya kawo shawaran a dinga kunna mun karatun Al'kur'ani ina saurara.

Na kai 2weeks a gidan Dadda ana mun magani, kuma alhamdllh an fara gani sauyi sosai, domin kwanana tara ina wannan hayaƙin jinin ya ɗauke,  yanzu abun da yake ɗan damuna shine rashin ƙarfi a jikina, wasu mafarke da bana iya tunasu idan na tashi, sai kuma rashin son dogon magana,  a haka muka cika sati uku cif, sai A.G ya dazo,  wannan zuwan tare da M.G suka zo, amma Heedayah an barta a chan, gaba ɗaya A.G yayi wani iri da shi, daga ka ganshi kaga baya cikin kwanciyar hankali, duk sai tausayin shi,  da son shi suka  cika zuciyata, suk inda yayi idona da hankalina suna kanshi,  bayan na idaar da sallan ishaa ne naji Dadda tace na haɗa kayana nabi mijina idan ya dawo daga masallaci,  ban ɓata lokaci ba kuwa na haɗa kayan wuri ɗaya,  saida suka shigi shida Alhaji tukun muka musu sallama muka tafi, bayan Alhaji  yayi mana dogon nasiha da shawarwari akan riƙo da ibadah,  sannan aka ja kunnena akan shan magunguna na.


Muna shiga gidanmu nagan shi fes yana tashin ƙamshi,  kallon A.G nayi da aman tambaya a fuskana,  murmushi yayi yana dubana da kyawawan lumsassun idunan shi yace,  "gaggawa da ɗoki irin na sabon ango yasaka nazo da wuri na gyara gidan, hafsy naje na ɗauko ta gyara miki ɗakunan da toilets ɗinki,"   murmushi nayi kawai na wuce hanyar nawa ɗakin, ina jin shi a baya yana biye da ni,  tsaf kuwa nasamu ɗakin da toilet ɗin, kallo na yayi yace,  "Eeshaa bari naje nayi wanka na dawo, kafin nan ma kema kinyi wankan, sai nazo musha maganin ko"?  Murmushi na mishi kawai bance komai ba, bayan ya fice a ɗakin ne n shige toilet nayi wanka, shiryawa na farayi sai gashi ya shigo, magunguna na ya ɗauko mun dukka nasha, sannan na shafa na shafawa, magic charcol ya kunna nayi hayaƙi na, ina ganin shi yana ta hatishawa saboda asthman shi da baya son hayaƙi, bayan a gama na zauna warin hayaƙin ya ɗan bar jikina kaɗan, chan na ɗauƙo humrah zan shafa naji ya riƙe hannuna,  "beauty yyh kuma da ɗauko turare"?  Kallon shi nayi jiki a sanyaye nace,  "zan sakane kada warin hayaƙin ya dameka",  lumshe ido yayi ya ɗan buɗesu kaɗan yace,  "hakan bazai yiwuba baby, idan Allah ya bamu lafiya zamuyi karaƙin shafa duk turare da muke so,amma yanzu kam ni  *AMINULLAHI GARBA INUWA* na yafe, a haka nake son Eeshaa ta, kuma ni ƙamshin ki nake ji a haka.


Allah sarki har na tuna da *AMINU MUHAMMAD BELLO ZARIA*
UMMI YAWALE
AI YAWALE
ZAINAB YAWALE
FATIE YAWALE
INDO YAWALE
kunta Aminu muhammad bello?
Idan ku tuna shi tou wannan page kyautane gareku ƴan'uwa na 
kutana ɗakin ƙarshe lokacin da nake reea waƙan soyayyah wa ɗan mutanen zaria 


*AUNTY NICE*