'Yan bindiga sun tilasta wa mazauna wasu yankunan Sokoto gudun hijira

'Yan bindiga sun tilasta wa mazauna wasu yankunan Sokoto gudun hijira
'Yan bindiga sun tilasta wa mazauna wasu yankunan Sokoto gudun hijira
'Yan bindiga sun tilasta wa mazauna wasu yankunan Sokoto gudun hijira
Mazauna karamar hukumar Sabon Birni a Jihar Sokoto na rayuwa ne a cikin bakin ciki sakamakon hare-hare, da ɓarnar da ‘yan bindiga ke yi wa  ƙauyukan dake makwabtaka da su.
Rahotanni sun nuna cewar, makwanni biyu da suka gabata ne ‘yan bingan suka dinga shiga kauyukan, tare da kashe akalla mutane dubu hamsin, da sace shanu.
Sakamakon wannan hare-haren dubban mata dake karamar hukumar Sabon Birni sun yi gudun hijira zuwa sakatariyar karamar hukumar, da makarantar firamari na Abdulhamid dake Sabon Birni.
Jaridar Daily Trust ta wallafa labarin dake cewa, da yawa daga cikin wadannan ‘yan Gudun hijiran sun koma Tudun Sunnah a jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, yayin da akwai wasu ‘yan gudun hijiran da yawa, da suka so tafiya kasar  ta Nijar, amma baza su samu damar tafiya ba, sabo da wasu dalilai.
Honarabul Gatawa a hirarsa da Managarciya ya tabbatar da mutanen yankinsu suna gudun hijira a ƙasar Nijar kuma mutanen na cikin damuwa suna buƙatar taimakon gwamnati a halin da suke ciki.
Ɗaya daga cikin 'yan majalisar dokoki a ƙaramar hukumar Sabon Birni Honarabul Aminu Boza ya yi faɗi tashin ganin an ɗauki matakin da yakamata ga mutanen da yake waƙilta.
Boza ya tafi in da 'yan gudun hijirar suke ya kai masu gudunmuwar kayan abinci da sauran buƙatun yau da kullum.