Zanga-zanga: Gwamnatin Kano ta fara bincike kan harin da aka kai wa babbar Kotun jihar

Zanga-zanga: Gwamnatin Kano ta fara bincike kan harin da aka kai wa babbar Kotun jihar

Zanga-zanga: Gwamnatin Kano ta fara bincike kan harin da aka kai wa babbar Kotun jihar

Ma'aikatar Shari'a ta Jihar Kano ta ce ta fara bincike domin tattara bayanan kadarorin da ɓatagari suka lalata tare da sacewa  a yayin zanga-zanga a jihar Kano a ranar 1 ga watan Agusta.

Mai magana da yawun kotuna, Baba Jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Lahadi.

Ya ce Babbar Kotun jihar Kano za ta fitar da rahoton irin barnar da aka yi nan bada jimawa ba.

Ya yi bayanin cewa ɓatagari, da sunan zanga-zanga sun kai hari kan babbar kotun, inda su ka sace kudade masu yawa da bindigar da aka samo daga masu garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa an kone motocin dake ajiye a bakin harabar babbar kotun tare da lalata ofishin  babbar alkaliyar jihar.

"Masu zanga-zangar sun lalata takardun shari'o'i sabbi da tsofaffi. Sun yi dai-dai da komai a ginin".

Baba Jibo ya kara da cewa wannan ne karo na farko da fannin shari'a ya fuskanci irin wannan barna daga ɓata gari.