Yadda Matashi ya haɗu da ajalinsa a lokacin da yake wankan cikin tafki a Kano
Yadda Matashi ya haɗu da ajalinsa a lokacin da yake wankan cikin tafki a Kano
Daga Ibrahim Hamisu
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta ce jami’anta sun tsamo wani yaro mai shekaru 15 mai suna Halifa Abdulmumini da ya nitse a wani tafki da ke Ƙauyen Dutsu a ƙaramar hukumar Gaya.
Hakan na cikin wata sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar SFS Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a yammacin jiya Juma’a.
sanarwar ta ce ofishin hukumar da ke ƙaramar hukumar ta Gaya ne ya samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Malam Isah Alhassan da misalin ƙarfe 1:42 na rana, inda kuma jami’an aikin ceto suka isa wurin da ƙarfe 2:10.
Sai dai bayan an ciro matashn daga ruwan ne cikin mawuyacn hali daga bisani aka tabbatar da rasuwarsa.
Kazalika sanarwar hukumar ta ce, tuni ta miƙa gawar sa ga Dagacin yankin na Dutsu Malam Lawan Habibu.
Lamarin ya ɗaga hakalin jama'ar wurin ganin yanda wannan matashin ya rasa ransa kai tsaye a wurin da 'ya'yansu ke zuwa domin wanka ko wata lalura ta yau da kullum.
Jami'an kashe gobara sun yi ƙoƙari matuƙa ganin yanda abin ya zo da kuma yanda suka yi a tsamo matashin duk da bai rayu ba a baya.
managarciya