Tsaro a Zamfara:Gwamnati ta hana babura yawon dare a dukkan faɗin jihar
Gwamnatin Zamfara ta dauki kwararan matakai domin magance matsalar tsaro.
Daga Aminu Abdullahi Gusau
Gwamnatin jihar Zamfara ta dauki kwararan matakai don magance matsalar kalubalen tsaro da ke addabar jihar.
Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a gidan gwamnati dake Gusau, babban birnin jihar.
Gwamna Matawalle, ya ba da umarnin rufe dukkan kasuwannin mako -mako a fadin jihar, ya ce dukkan babura su yi aiki tsakanin karfe shidda na safe zuwa shidda na yamma a duk kananan hukumomin jihar ban da karamar hukumar mulkin Gusau ita an ƙara mata awa biyu 6:00am zuwa 8:00 na dare, kuma rashin biyayya na iya haifar da harbi akan wanda ya bijera ma dokan.
Gwamnan dai ya ba da umarnin cewa ba a yarda babur ya dauki mutum uku ba, sai dai babur din da aka fi sani da keke napep. Hakama za'a ci gaba da bankado haramcin sayar da man a cikin jarkoki da kwantena.
A cewarsa duk wuraren da ake sayar da giya, miyagun kwayoyi da sauran abubuwa masu guba a cikin jihar a rufe su nan ba da jimawa ba za a kaddamar da kwamiti na aiki don aiwatar da dokokin.
managarciya