Abaiwa Mata Ilmi Su Fahimci Kalubalen Da Ke Gabansu----Dakta Aisha Balarabe Bawa

“Kamar yadda na fada a farko abu ne da ya shiga cikin jinin mutanenmu ba a arewa kadai ba, abu ne da ya mamaye duniya koyaushe namiji na ganin shi ne gaba mace tana kasa don mi za ta yi gwagwarmaya da namiji duk da matan ne, ke da kashi 50 na mutanen duniya kuma suna iya kawo cigaba ta bangarensu, ja bayansu na kawo cikas a tattalin arzikin kasa da ilmi da mulki, aba su dama ba yana nufin mace ta zama kamar namiji ba, ko ta yi kafada da shi, mazan sun ki yarda su aminta su baiwa mace damar da addini ya ba ta, a neman ilmi da bayar da gudunmuwa. Ana sanya addini da al’ada wajen kange su ba su samun isasshen ilmi da arziki da karbuwa, an sanya  musu tsoro da rauni sun yarda ba su iyawa, su matan sun ki la’akari duk abin da aka ce ba su iyawa sun zo sun yi shi sun wuce wurin tun tuni.” Kalaman Dakta kenan.  Dakta Aisha Bawa ‘yar asalin jihar Kebbi ce da ta yi dukkan karatunta a Sakkwato, ta ce  “Mijina ya bani gyon baya dari bisa dari, don yasan abin da nake yi abu ne na taimakon al’umma.”

Abaiwa Mata Ilmi Su Fahimci Kalubalen Da Ke Gabansu----Dakta Aisha Balarabe Bawa

 Daga Sadiya Attahiru

 

Dakta Aisha Bawa mace ta farko a matsayin Mataimakiyar shugabar Kungiyar Malamai ta jami’ar Usman Danfodiyo da ke jihar Sakkwato, daya daga cikin jagorori a fannin  nazarin ilmin tarihi na Nijeriya, tana cikn mata kalilan da suka yi karbar sakamakon zaben 2015, ta yi tafiye-tafiye kan harkar ilmi a kasashen Turai. Mace mai gaskiya da rikon Amana da son cigaban al’ummarta musamman mata, tana aiki tutukuru don samar da al’umma ta gari.

Dakta Aisha a zantawarta da Managarciya ta yi magana kan mukaman da ta rika “Lalle akwai gwagwarmaya a shugabancin kungiyar malamai na jami’a  a hannun mace abu ne da ake kallo sabo a lokacin da aka bani mukamin, kasancewa a Arewacin Nijeriya ba a cika ganin mata suna gwagwarmaya da maza a harkar shugabancin kungiya ba, musamman wanan da ke fafutikar nemawa malamai hakkinsu da tabbatar  da ingantuwar ilmi a kasa baki daya.  Ina da ra’ayi ga abin da ya shafi kwatanta gaskiya da nemawa mai hakki hakkinsa musamman talakawa da mata,  haka ya sanya na yi aiki da kungiyoyi masu zaman kansu”.

“A wannan yanki namu naga kamar mata ba su bayar da muhimmanci  a wajen gwagwarmaya domin rashin ba su dama, dubi siyasar Nijeriya za ka ga ba su da yawa,  an saka al’ada da amfani da addini a danniyar ta  maza, ba su baiwa mata hakkinsu a wajen gudanar da mulki yana cikin abin da ke kara kawo cikas ga cigaban mata har a jami’o’i amma yanzu abin ya fara gushewa har an samu mace shugabar jami’ar Jigawa.” A cewar Dakta Aisha.

Da ta koma kan abin da ya karfafata ta ce  “Na samu goyon baya don ita mace duk abin da za ta yi in ba ta samu hadin kan maza ba, sun ba ta dama to abun ba zai yi wu ba. A harkar kungiya Farfesa Sule Kano ya karfafani ya bani dama aka sanni da rawar da nake iya  takawa a kasa, na yi aikace-aikace har shirya zabe da taruka, kasancewar hakan ne ya sanya na dawo gida yankina don muna da gibin mata a shugabannin kungiya, sai aka neme ni na zama mataimakiyar ciyaman na aminta, na yi haka ne don mata su tabbatar suna iyawa ba da ta su gudunmuwa, kuma sai   na rika janyo mata ina  sanya su cikin kwamitoci in za mu yi horaswa na NDC da wasu wuraren, akwai wani horaswa da ake  bukatar mutum 50 na sanya mata 15 a ciki, a yanzu ko bani nan na tabbata an samu mata da  za su iya cigaba da in da na tsaya. Abu ne da muke bukata in mace ta samu ta jawo ‘yan uwanta su samu, mu bar adawa da jin haushin junanmu.” In ji ta.

Wakiliyarmu ta nemi ta kara bayani kan kwarin guiwa da jajircewar mata, don har yau ba’a ganin mata na iya bayar da gudunmuwa a waje.

“Kamar yadda na fada a farko abu ne da ya shiga cikin jinin mutanenmu ba a arewa kadai ba, abu ne da ya mamaye duniya koyaushe namiji na ganin shi ne gaba mace tana kasa don mi za ta yi gwagwarmaya da namiji duk da matan ne, ke da kashi 50 na mutanen duniya kuma suna iya kawo cigaba ta bangarensu, ja bayansu na kawo cikas a tattalin arzikin kasa da ilmi da mulki, aba su dama ba yana nufin mace ta zama kamar namiji ba, ko ta yi kafada da shi, mazan sun ki yarda su aminta su baiwa mace damar da addini ya ba ta, a neman ilmi da bayar da gudunmuwa. Ana sanya addini da al’ada wajen kange su ba su samun isasshen ilmi da arziki da karbuwa, an sanya  musu tsoro da rauni sun yarda ba su iyawa, su matan sun ki la’akari duk abin da aka ce ba su iyawa sun zo sun yi shi sun wuce wurin tun tuni.” Kalaman Dakta kenan.

 Dakta Aisha Bawa ‘yar asalin jihar Kebbi ce da ta yi dukkan karatunta a Sakkwato, ta ce  “Mijina ya bani gyon baya dari bisa dari, don yasan abin da nake yi abu ne na taimakon al’umma.”

“Abaiwa mata ilmi su fahimci kalubalen da ke gabansu su kuma san duk abin da za su yi kasa suke ga maza, ba wata mace da ta zama wani abu; ba mijinta ne ya taimaka mata ba, mata uwaye ne masu tausayi  samunsu alheri ne a gida, a rika daga masu ana janyo su a jiki, ga abin da ya shafi aikinsu na cigaban al’umma. Mace ba baiwa ba ce, abokiyar zama da shawara ce, musulunci bai yarda maza su tauye hakkin matansu ba, ya ba ta dama ta mallaki kudin kanta ta hanyar yin sana’o’in da shari’a ta aminta da su, in mace ta zama tana da nata zai kara taimakon aurenta da iyalinta.” Dakta Aisha kenan.